Rundunar ‘yansandan jihar Edo sun samu nasarar kashe uku daga cikin gungun mutum shida na ‘yan garkuwa da mutane, wadanda suka sace wani yaro dan wata 13 a yankin Achigbor da ke kan layin Benin zuwa Auchi a karamar hukumar Uhunmwonde da ke jihar.
A wata sanarwar manema labarai da mataimakiyar jami’in watsa labarai na hukumar ASP Jennifer Iwegbu ta fitar a ranar Laraba, ta ce, mahaifiyar yaron Elizabeth Ojo ce ta tsegunta musu batun garkuwa da yaron nata inda suka tunkarar masu garkuwa hadi da ceto yaron a galabaice.
Ta ce, wannan matakin na daga cikin kokarin rundunar na dakile aniyar bata-gari a fadin jihar ne.
“Lamarin ya faru ne a ranar Talata, cikin gaggawa rundunarmu ta hada kan jami’ai suka je inda abun ya faru. Zuwan Jami’anmu wurin ke da wuya muka tarar an yi kaca-kaca da wurin. Ita Ojo ya shaida mana cewa wasu ne dauke da makamai suka lalata mata kadarori tare da yin garkuwa da danta dan watanni 13 inda suka gudu da shi cikin daji.
“Ba tare da wata-wata ba, ‘yansandan suka kutsa kai cikin dajin da nufin ceto yaron. Masu garkuwan suna jin isowar ‘yansandan suka bude musu wuta. A artabun da suka yi da ‘yansanda, uku daga cikin shida na masu garkuwan sun tafi lahira bayan da ‘yansanda suka sha karfinsu. Sauran ukun sun gudu cikin daji amma ana cigaba da bincikosu.’
Sanarwar ta an ceto yaron tare da mika shi ga mahaifiyarsa, Kuma sun kwato bindiga da adda daga wajen masu garkuwan a lokacin da suka tunkaresu.
Ta kara da cewa, kwamishinan’yan sandan jihar CP Abutu Yaro, ya jinjina wa kokarin jami’ansa na Kai daukin gaggawa, ya nemi al’ummar jihar Edo da su cigaba da baiwa ‘yansandan hadin kai da basu bayanan abubuwan da suke faruwa domin daukan matakan da suka dace.