Rundunar ‘yansandan Jihar Delta ta ce ta kashe wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne da garkuwa da mutane a karamar hukumar Udu da ke jihar.
Kakakin rundunar, DSP Bright Edafe ne, ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Litinin a Warri.
- Wannan Sabuwar Tashar Jirgin Ruwa Ta Shaida Wani Tunani Mai Muhimmanci
- Jirgin Kasan Kaduna-Abuja Ya Dawo Aikin Jigilar Fasinjojinsa Bayan Hatsarin Da Ya Yi
Edafe ya ce jami’an ‘yansanda da ke ofishin ‘yansanda na Ovwian/Aladja sun kashe su ne a ranar Alhamis.
Ya yi bayanin cewa jami’in ‘yansanda na yankin, CSP Aliyu Shaba ya samu sahihan bayanai cewa an ga wasu ‘yan fashi da makami da garkuwa da mutane guda biyu a wani gidan casu.
“Cikin gaggawa DPO ya jagoranci ‘yansanda zuwa wurin inda aka kama daya daga cikin wadanda ake zargin. Nan take wanda ake zargin ya amsa cewa shi mamba ne na kungiyar ‘yan fashi da makami da garkuwa da mutane.
“Wanda ake zargin, daga nan ne ya jagoranci ‘yansandan zuwa maboyarsu da ke Udu inda ‘yan fashin suka yi artabu da ‘yansanda.
“A yayin artabun, jami’an ‘yan sanda sun kashe daya daga cikin wadanda ake zargin. Sannan sun kama daya bayan ya samu munanan raunuka sakamakon gobarar da ta tashi yayin da sauran ‘yan kungiyar suka tsere.
“Wanda ake zargin ya mutu kafin a karasa da shi asibiti. Ana ci gaba da farautar sauran da suka tsere,” in ji shi.
Edafe ya ce an kwato bindiga kirar AK47 daya da alburusai 27 daga wurin.
Ya ce, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ari Ali ya tura rundunar zuwa Oghara don gudanar da bincike.