Rundunar ‘yansandan Jihar Anambra da hadin guiwar sojoji sun yi nasarar kashe wasu da ake zargin ‘yan kungiyar masu rajin kafa kasar Biyafara ne guda uku tare da kama wasu biyu.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun DSP Tochukwu Ikenga, kakakin rundunar ‘yansandan jihar, kuma ya bayyana wa manema labarai a Onitsha a ranar Litinin.
- ‘Yansanda Sun Cafke Wasu Mutum 3 Kan Zargin Mallakar Kudaden Jabu A Jihar Kebbi
- Kasashe Masu Tasowa Sun Zargi Kasashen Yamma Da Nuna Jahilci
A cewarsa, da misalin karfe 02:20 na dare wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar IPOB ne sun kai hari a ofishin ‘yansanda na Awada da ke karamar hukumar Idemilli ta Arewa a Anambra, inda suka yi amfani da abubuwan fashewa da kuma bindigogi wajen kai harin.
“A matsayin martani ga harin, jami’an ‘yan sanda sun yi artabu da bindigar tare da kashe wasu guda uku.
“An kwato bindigogi guda uku daga hannunsu.
“An kwato mota kirar Lexus 330 mai launin ruwan kasa mai lamba. GWA 415BB ABJ, babur kirar KYMCO mara rijista da ake zargin na sata ne, laya da sauran kayan tsafi.
“A yayin wani samame da jami’an ‘yansanda da sojoji suka kai, an kama wasu maza biyu da ake zargi da hannu a harin.
“Sai dai, ‘yansanda hudu sun rasa rayukansu yayin harin da suka kai yankin.”
Sanarwar ta kara da cewa, Kwamishinan ‘yansandan jihar, Mista Echeng Echeng, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan faruwar lamarin.
Echeng ya kuma yi kira ga mazauna garin Awada da mutanen Jihar Anambra da su kwantar da hankalinsu domin ‘yansanda tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro za su gurfanar da masu laifin da suka addabi Jihar..