Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta kuɓutar da wasu matasa 19 ‘yan ƙasar Ghana da aka shigo da su ƙasae ta hanyar yaudara, da sunan za a ba su aiki.
Wata sanarwa daga rundunar ‘yansandan Jihar Oyo ta bayyana cewa an gano mutanen ne a Ibadan, bayan samun sahihan bayanan sirri daga jama’a.
- Namadi Sambo Ya Yaba Wa Gwamna Abba Yusuf Kan Bunƙasa Ɓangaren Ilimi Da Gine-Gine A Kano
- Za A Fara Sufurin Ma’aikata Da Ɗaliban Kaduna Kyauta A Bas
Kakakin rundunar, Adewale Osifeso, ya ce cikin waɗanda aka kuɓutar akwai maza 14 da mata biyar, kuma an shigo da su ne da tunanin za a ba su aikin yi.
Ana zargin cewa wasu da ke safarar mutane ne suka kawo su Nijeriya don amfana da su.
Yanzu haka, an miƙa matasan ga Hukumar Shige da Fice domin ci gaba da bincike, kuma ana sa ran za a mayar da su Ghana bayan kammala binciken.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp