Rundunar ‘Yansanda a jihar Nasarawa, ta tabbatar da yin garkuwa da wata dalibar kwalejin Kimiyya da fasaha ta Mustapha Agwai da ke a garin Lafia babban birinin jihar.
Kakakin rundunar, DSP Ramhan Nansel, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwar da ya fitar.
- Cunkoso A Gidan Yari: Yadda Mutum 1400 Ke Zaman Jiran Shari’a A Nasarawa
- Gwamnan Nasarawa Ya Bukaci Kotu Ta Yi Watsi Da Karar Dan Takarar Gwamna Na PDP
An ruwaito cewa, dalibar wadda take zangon karatu na biyu a kwalejin a sashen kimiyya da fasaha na kwalejin.
Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan bindigar sun kutsa cikin kwalejin, inda suka harbe dalibai uku da suka hada da Freedom Luka da ke zangon karatu na daya a sashen koyon darasin mulki.
Sai kuma Ogwuche Janet da ke a zangon karatu na karshe a sashen koyon darasin kasuwanci da kuma Danlandi Nicholas da ke a saahen koyon ilimin tattalin arziki, sai kuma daliba guda da aka sace.