Rundunar ‘yansandan Jihar Adamawa, ta ce jami’anta sun kama wasu mutane biyar da ake zargin masu garkuwa da mutane ne.
Ta kuma kara da cewa jami’an sun kwato kudi Naira miliyan 4,079,000 daga hannun wadanda ake zargin.
- ‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga 2, Sun Kwato Makamai
- Gwamnatin Kogi Ta Bai Wa Dangote Sa’o’i 48 Ya Kulle kamfanin Simintinsa Da Ke Obajana
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan jihar Adamawa, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya fitar ranar Juma’a.
A cewar sanarwar, jami’an rundunar, a ranar 9/10/2022, sun katse wata hanyar sadarwa da ke da alaka da kungiyoyin ta’addanci guda biyar a kananan hukumomin Mubi ta Arewa da Kudu.
Rundunar ta ce jami’an sun samu rahoton yin garkuwa da wani matashi mai suna Mustapha Aliyu Fadil dan shekara 8 a garin Mubi tare da kai shi otal din Barassa da ke Maraba Mubi.
Ya ce nan take rundunar ta tattara jami’anta da ke da alaka da Hukumar Leken Asiri ta Jihar (SIB) suka gudanar da aikin, an kuma yi nasara.
A cewarsa, an samu nasarar kwato makudan kudi har miliyan hudu da da dubu saba’in da tara daga cikin Naira miliyan biyar, da aka biya a matsayin kudin fansa.
Ya ce wadanda ake zargin sun hada baki ne suka tafi da wanda suka sace inda suka tsare shi har na tsawon kwanaki biyu har sai an biya su kudin fansa miliyan biyar kamar yadda suka nema kafin a sako wanda abun ya shafa.
A cewarsa, kwamishinan ‘yansandan, SK Akande, yayin da yake yabawa jami’an bisa yadda suka katse hanyoyin sadarwa ta hanyar nuna kwarewa, ya umarci jami’an da su ci gaba da gudanar da irin wannan aikin, a matsayin dabarun binciken laifuka da masu aikata laifuka a cikin jihar da kewaye.
“CP ya yi kira ga jama’a da su sanar da ‘yansanda a ko da yaushe game da inda masu laifi suke da maboyarsu, musamman ma wadanda ke da ake da kokwanto a kan su,” in ji shi.