Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Josh Kroenke, ya shaidawa kocin kungiyar, Mikel Arteta cewa, lokaci ya yi da zai lashe kofin gasar Firimiyar kasar Ingila.
Arsenal na daya daga cikin manyan kungiyoyin wasanni mallakar Kroenke Sports and Entertainment (KSE), gaba daya kungiyoyin wasanni da Kroenke ya mallaka sun lashe kofuna hudu a cikin watanni 18 amma babu Arsenal a jerin wadanda suka lashe kofuna.
A cewar jaridar Mail Sport, Josh Kroenke ya aika wa Arteta da wasika, inda yake gaya masa cewa, lokaci ne da ya kamata Arsenal ta lashe kofin gasar Firimiya duba da yadda ya subuce mata a kakar wasanni biyu na baya-bayan nan.
Arsenal wadda Arteta ke jagoranta sun kare a matsayi na biyu inda Manchester City ta lashe duka kofunan a cikin shekaru biyun da suka gabata, rabon da Arsenal ta lashe gasar Firimiya tun shekarar 2005 a lokacin Arsene Wenger na koci.