Wasu ƴan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun afka garin Dogon Ruwa da ke ƙaramar hukumar Wase a Jihar Filato, inda suka sace miji da matarsa da ɗansu. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na safe a ranar Litinin, yayin da maharan suka dira ƙauyen, suna harbe-harbe domin tsoratar da jama’a kafin su tafi da mutanen da suka sace.
Majiyoyi daga yankin sun tabbatar da cewa wasu mutane biyu sun ji raunuka sakamakon harbin bindiga, kuma an garzaya da su zuwa asibiti domin samun kulawa. Shugaban matasan yankin, Shapi’i Sambo, ya bayyana cewa jami’an tsaro da ‘yan sa-kai sun shiga daji don ceto waɗanda aka sace.
Harin ya ƙara jefa jama’ar yankin cikin fargaba, duba da yadda sace-sacen mutane ke ci gaba da ƙaruwa a wasu sassan Jihar Filato. Sai dai har zuwa lokacin da ake haɗa wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan jihar ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.
Mutanen yankin sun bukaci gwamnati da hukumomin tsaro su ɗauki matakan gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da daƙile hare-haren ‘yan bindiga a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp