Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa (ASUU) ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na ƙasa baki ɗaya na tsawon mako biyu daga daren Litinin, 13 ga Oktoba, 2025.
Shugaban ƙungiyar, Farfesa Chris Piwuna, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a cibiyar ASUU ta ƙasa da ke Jami’ar Abuja, inda ya zargi gwamnatin tarayya da rashin gaskiya wajen tattaunawa kan buƙatun ƙungiyar.
- Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shirin Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu
- ASUU Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwanaki 14 Don Biyan Buƙatunta
Piwuna ya ce gwamnati ta gaza cika Alƙawurran da ta ɗauka duk da sanarwar kwanaki 14 da ASUU ta bayar tun a ranar 28 ga Satumba, 2025. Ya ce babu wani abin da aka cimma wanda zai hana ƙungiyar aiwatar da shawarar majalisar zartarwarta (ASUU-NEC) na fara yajin aikin.
“Dukkan rassan ASUU a faɗin ƙasar nan an umarce su da su janye ayyukansu daga misalin ƙarfe 12 na dare ranar Litinin,” in ji Piwuna, yana mai bayyana cewa makonni biyun na yajin aiki za su zama dama ta ƙarshe ga gwamnati don kammala tattaunawar da ƙungiyar.
Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta kasa magance matsalolin cikin wannan lokaci, za ta ɗauki mataki mafi tsanani bayan kammala yajin aikin gargadi.