Everton ta kulla yarjejeniya da dan wasan Aston Villa Ashley Young kan kwantiragin shekara guda bayan dan wasan bayan ya bar Aston Villa a bazara.
Young mai shekaru 38, ya zama dan wasa na farko da Everton ta saya a karkashin sabon kocinta Sean Dyche.
BBC ta ruwaito cewa Young ya tattauna da Luton town yayin da kuma akwai sha’awar sayensa daga kungiyoyin Saudiyya.
Tsohon dan wasan Ingila Young ya ce “Na yi farin cikin zama dan wasan Everton da kuma shiga wannan babbar kungiyar.
A watan Janairu ne tsohon kocin Burnley Dyche ya maye gurbin Frank Lampard da aka kora.
Dyche ya jagoranci kungiyar ta yi nasara a gasar Firimiya League a ranar karshe ta kakar wasanni.
Dyche ya ce Ashley babban kwararre ne wanda tarihin kungiyarsa da nasarorin da ya samu a lokacin da ya yi nasara ya sa ya zama abin alfahari a cikin tawagarmu.
Na san Ashley shekaru da yawa, kasancewar ya kasance kyaftin dina a lokacin da ina horarwa a Watford.
Kuma halayensa a cikin fili da wajen fili za su tabbatar da muhimmancinsa a harkar kwallon kafa.
Young mai tsaron baya ya lashe gasar cin kofin Europa da League Cup tare da Manchester United kuma ya buga wa Ingila wasanni 39.
Young ya buga wasanni sama da 700 a kulob da kuma kasa ciki har da wasanni 32 da ya buga wa Villa a kakar wasan da ta wuce.
Young ya kara da cewa na san abubuwa ba su yi wa Everton kyau sosai ba a cikin shekaru biyun da suka gabata.
Everton babban kulob ne kuma magoya bayansa na daya daga cikin mafi kyau. Samun su a bayana wata dama ce mai ban sha’awa.
A koyaushe na ce shekaru lamba ce kawai a gare ni, tsufa ba zai hana ni wasa mai kyau ba.
A ranar Litinin ‘yan wasan Toffees sun tafi Switzerland don yin atisayen kwanaki biyar a tsaunukan Alps. Inda za su kara da kungiyar Stade Nyonnais a wasannin sada zumunci.
Na Yafe Wa Kowa, Ina Rokon Yafiyar Kowa —Sheikh Dahiru Bauchi