Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya lashe zaben da aka gudanar a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, 2023.
Diri ya samu nasarar ne bayan tattara sakamakon zaben daga dukkan kananan hukumomi takwas na jihar a ranar Litinin da yamma.
- Da Dumi-dumi: Ododo Na APC Ya Lashe Zaben Gwamnan Kogi
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 3 Da Kwato Makamai A Kaduna
Jami’in kula da zabe na jihar, Farfesa Faruq Kuta, da misalin karfe 12:42 na ranar Litinin, kimanin sa’o’i 48 da zaben da aka gudanar a jihar Kudu-maso-Kudu mai arzikin man fetur, ya bayyana cewa, zaben ya zo karshe.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, Gwamna Diri ya lashe zabe a kananan hukumomi shida daga cikin takwas na jihar, yayin da babbar jam’iyyar hamayyarsa, APC da dan takararta Timipre Sylva ya lashe kananan hukumomi biyu kacal.
Kananan hukumomin jihar dai, sun hada da Kolokuma/Opokuma, Ogbia, Yenegoa, Sagbama, Nembe, Ekeremor, Brass, da Kudancin Ijaw.
Dan takarar PDP ya lashe zaben ne da tazarar kuri’u 65,088 a tsakaninsa da dan takarar jam’iyyar APC.