Jami’an tsaron kasa da kasa (Interpol) sun cafke babban jami’in kamfanin Kirifto na kamfanin Binance, Nadeem Anjarwalla, wanda ya tsere daga hannun hukumomin tsaro a Nijeriya.
A cewar ‘yansandan Kenya, sun kama Nadeeem Anjarwalla ne a kasa kuma suna shirin mika shi zuwa Nijeriya domin fuskantar shari’a.
- Uba Da Ɗa Sun Mutu Wajen Ciro Waya A Masai A Kano
- Ba Zan Taba Iya Aure Ko Zama Da Wanda Ba Ya Son Sana’ar Dana Ke Yi Ba -Asmee Wakili
Wani daga gwamnatin kasar da ya nemi a saka sunansa, ya tabbatar da kamen a ranar Lahadi.
“Jami’in Binance, Nadeem Anjarwalla ya shiga hannun ‘yansandan Kenya, kuma wannan satin Interpol za su mika shi Nijeriya,” in ji majiyar.
Idan ba a manta ba Nadeem Anjarwalla ya tsere daga hannun hukumomin tsaron Nijeriya ne a yayin da yake fuskantar shari’a kan ayyukan kamfaninsa da gwamnatin kasar ta haramta, kan alakar Binance da tashin Dalar Amurka.
Kazalika, gwamnatin Nijeriya na tuhumarsa da rashin biyan haraji da kuma almundahanar kudi har Dalar Amurka miliyan 35,400,000.