Babban daraktan hukumar kula da lafiya a matakin farko ta kasa (NPHCDA), Dakta Muyi Aina, ya ce, har yanzu mata da dama na rasa rayukansu a Nijeriya sakamakon juna biyu da kuma wurin haihuwa, sannan kuma jarirai da dama ba su samun zarafin kai wa shekaru biyar a duniya sakamakon cuttukan da aka kasa shawo kansu.
Aina ya shaida hakan ne a ranar Litinin a Abuja a wajen taron wayar da kai kan rigakafi da batutuwan kula da lafiyar mata da yara wanda gidauniyar Sultan ta fadi tashin wanzar da zaman lafiya (SFPD) da hadin gwiwar NPHCDA suka shirya wa shugabannin addini daga yankin arewacin Nijeriya.
- Jami’an Tsaro Sun Ceto Manoma 6 Da Aka Sace A Katsina
- EFCC Ta Kama Tsohon Gwamnan Taraba Ishaku Kan Zargin Badaƙalar 27bn
Shugaba NPHCDA ya kuma kara da cewa Nijeriya ta samu kesa-kesai 70 na kara-min cutar foliyo Type 2 daga kananan hukumomi 46 a jihohin arewacin Nijeriya 14, inda ya ce an samu wannan ne sakamakon rashin yin rigakafi a kai a kai, yayin da wasu kuma ke kin amsar rigakafin foliyo a lokacin da ake gangamin wayar musu da kai.
“A kowace rana, Nijeriya tana rasa sama da yara ‘yan kasa da shekara 5 guda 2,300 da kuma rasa iyaye mata 145 masu dauke da juna biyu a wajen haihuwa. Dukkanin wadannan mace-macen na faruwa ne a yankin arewaci.
“Dole ne a canza wannan matsalar. Dole mu tabbatar kowace mace na sun zuwa awo da kuma kulawar da suka dace, kowace mace mai juna biyu ta haihu a han-nun kwararrun unguwar zoma, kuma kowani yaro ya samu damar kammala am-sar rigakafin kamar yadda yake kunshe cikin tsarin kasa, kuma a tabbatar sun samu rigakafi a kowani lokaci a gidajensu. In muka hada hannu za mu cimma na-sarar zuwa matakin da babu wani yaro da za a bar shi ba tare da ya samu rigakafi ba.”
Aina ya bukaci shugabannin addini da su kara jan damara da himma domin ganin an samu inganta kiwon lafiyan jama’a. Ya ce, akwai bukatar a cire dabi’ar wariya wajen bayar da kiwon lafiya ga mutane tare da tabbatar da kowa na samun ku-lawar kiwon lafiya yadda ya dace.
Daga bisani ya jinjina wa Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, da babban Rabaran, Daniel Okoh bisa gayyato shugabannin addinai da sarakuna da suka yi domin samun wannan horon na musamman kan yadda za a kara wayar da kan jama’a game da muhimmancin rigakafi.