Matar marigayi shugaban kasar Nijeriya, Umaru Musa ‘YarAdua, Hajiya Turai ‘YarAdua ta bayyana cewa, mijinta bai taba son shugabantar Nijeriya ba, kuma bai taba matsawa sai ya zama ba.
Turai a wata hira da ta yi da BBC Hausa bayan cikar mijin nata shekaru 13 da rasuwar, ta sanar da cewa marigayin a lokacin yana raye, ba shi da sha’awar siyasa, amma za a iya danganta shi a matsayin dan siyasa na tsautsayi.
- Na Fi Son ‘Acting’ Na Masifa Don Na Fi Sabawa Da Shi – Sadiya Musa
- Batun Sake Nazarin Dakatar Da Tsohon Sarkin Kano…
Ta kara da cewa, burinsa shi ne ya zama malamin makaranta wanda kuma ya dawo gidansa ya zauna ya yi ta yin raha da iyalansa.
A cewarta, bai taba son ya shiga siyasa ko ya yi shugabanci ba, amma Allah da ikonsa ya shiga siyasa har ya zama shugaban kasa.
Ta sanar da cewa, ko a lokacin da ya zama shugaban kasa, rayuwarsa ba ta sauya ba, domin bai rungumi yin rayuwa mai tsada ba kuma mutum ne mai saukin kai.
Da ta ke yin magana kan rayuwarta da kuma yadda ta yi rashin mijin nata, ta bayyana cewa, tana tuna ‘YarAdua a kullum ba wai sai a ranar zagayowar tuna ranar rasuwarsa ba
Turai ta sanar da cewa, ina jin dadi duk lokacin da ranar tunawa da shi ta zagayo, domin ‘yan kasar nan na yin magana kan kyawawan halayensa
Da take tuna ranar da ya rasu ta ce, bayan ya kwanta jinya ta na yin Azumi a kulum, inda a waccan ranar ta 5 ga watan Mayun 2010, bayan an sha ruwan Azumi na rike hannaynsa na ce masa barci ya dauke ne baya an sha ruwa, inda ya giriza kansa.
Ta ce, bauyan ‘yan lukota an kira ni bayan na dawo, na iske ya rasu, inda ta kara da cewa, na yi danasani a wannan ranar na kuma zargi kaina saboda zuwa buda bakin Azumin, inda na yi tunanin mai yasa ban tsaya tare da shi ba.
A cewarta, amma na godewa Allah da ya bani Yar’adua a matsayin mijina, wannan babbar dam ace a rayuwa ta ina kuma godewa na kasance wani rabi na rayuwarsa.
Da take yin magana kan gwamati mai zuwa Turai kan matasar shugaban kasa mai jiran Gado, Remi Tinubu, ta shawarce da ta kasance mai haukuri da jurewa dukkan kalubalen da za ta ci karo da shi tare da taimaka wa mijinta don ya sauke nauyin da ke akansa.