An sako wasu yara 30 wadanda mafi yawansu mata ne da aka yi garkuwa da su a kauyen Kasai da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina.
An rahoto cewa, yaran an yi garkuwa da su ne yayin da suka shiga jeji domin samo itacen girki a ranar Litinin, hakan ya jefa al’ummar kauyen cikin fargaba matuka.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 11 A Katsina Da Zamfara
- Gwamnan Katsina Ya Raba Fiye Da Naira Miliyan 470 Ga Wadanda Ta’addancin ‘Yan Bindiga Ya Rutsa A Jihar
Sai dai kuma, kasa da sa’o’i 24, yaran sun shaki iskar ‘yanci daga wadanda suka yi garkuwa da su, sakamakon yunkurin gaggawa da jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki a cikin al’umma suka yi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq ne ya tabbatar wa kamfanin labarai na News Point Nigeria a ranar Talata.