A halin da ake ciki dai Ƙungiyar ƙwadago ta janye shirin shiga yajin aikin da za ta Jagoranta da za a fara a yau Talata.
An cimma wannan ci gaban ne sakamakon wata yarjejeniya da aka cimma tsakanin gwamnatin tarayya da ƙungiyoyin ƙwadago, wanda NLC ke jagoranta a wani zama da ya gudana a jiya Litinin a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
- DA DUMI-DUMI: Kotu Ta Tsige Gwamnan Nasarawa Na APC Ta Ayyana Umbugadu Na PDP
- Kotun Zaben Kano: DSS Ta Cafke Matar Da Ta Yi Wa Shettima, Gawuna Da Alkalin Kotun Barazana
Wasu daga cikin muhimman abubuwan da aka cimma a wannan yarjejeniya, sun haɗa da alƙawarin da gwamnatin tarayya ta yi na ƙarin N35,000 ga duk ma’aikata har na tsawon watanni shida daga watan Satumba.
Haka kuma, a cikin yarjejeniyar, akwai, “kafa wani kwamiti mai ƙarfi cikin wata ɗaya, wanda zai duba batun ƙarin albashi ga ma’aikatan ƙasar nan.
“Janye harajin da aka sanya a harkar man gas (Diesel) na tsawon watanni shida daga watan Oktobar 2023.

“Sanya Naira biliyan 100 don sayo manyan motocin bas-bas masu amfani da man gas na girki don sauƙaƙa wa jama’a hanyar zirga-zirga a duk faɗin ƙasar nan, wanda ake sa ran za a yi a watan Nuwambar nan.
Haka kuma an cimma yarjejeniyar ɗauke haraji ga wasu kamfanoni da ɗaiɗaikun jama’a don sauƙaƙa masu wajen hada-hadar yau da kullum.
Haka kuma an cimma yarjejeniyar sasantawa a ƙungiyar direbobi ta ƙasa ta NURTW, tare da sanya baki a batun soke ƙungiyar masu motocin hN25,000 a duk wata daga watan Oktobar nan ga ‘yan Nijeriya mutum Miliyan15, wanda ya haɗa da tsofaffin ma’aikata masu karɓar fansho.
Akwai kuma ƙara faɗaɗa shirin nan na rabon taki ga manoma a duk faɗin ƙasar.
An kumma cimma matsayar cewa su ma jihohi da Ƙananan Hukumomi, za a ƙarfafa masu gwiwa domin aiwatar da wannan ƙarin albashi ga ma’aikatan su.
“Samar da kuɗaɗe ga matsaƙaita da ƙananan masana’antu, sannan za a mayar da hankali wajen ƙirƙiro da ayyuka ga matasa.
Za kuma a fito da shirin zagaya matatun man fetur ɗin ƙasar nan don tantance irin gyaran da su ke buƙata.
Gwamnatin taraya za ta yi amfani da takardun da kotu ta sahhale ne wajen saka hannu akan wannan yarjejeniyar fahimtar juna cikin mako daya.
Ita dai wannan yarjejeniya ta samu sanya hannun shugaban NLC na ƙas, Joe Ajaero, Sakataren NLC, Emmanuel Ugboaja, shugaba da Sakatare na TUC, Festus Osifo da Nuhu A.
A ɓangaren gwamnatin tarayya, akwai Ministan Ƙwadago, Simon Lalong da Ƙaramin Ministan sa, Nkeiruka Onyejeocha da kuma Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris.