Kotun daukaka kara da ke da zama a Abuja, ta sanar da yau Talata, a matsayin ranar da zanta yanke hukunci tsakanin gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, da dan takarar kujerar gwamna a jam’iyyar SDP a zaben 2023, Dakta Umar Ardo.
A sanarwar yanke hukuncin, kotun ta ce yanke hukunci kan daukaka karar da Dakta Umar Ardo ya shigar, tsakaninsa da gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da wasu 3, zai gudana ranar Talata 21/11/2023″ in ji sanarwar.
Dakta Umar Ardo, na kalubalantar hukuncin da kotun sauraren koke-koken zabe da ta yi watsi da karar da ya shigar yana mai kalubalantar gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da hukumar zabe (INEC) da wasu 16.
Haka kuma Dakta Umar Ardo, ya nemi kotun daukaka karar da ta rushe hukuncin da kotun sauraren koke-koken zaban ta yanke.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp