Ana zaman dar-dar a Kano a daidai lokacin da babbar kotun tarayya a ƙarƙashin Mai shari’a Muhammad Liman ke shirin yanke hukunci kan soke dokar masarautar Kano. Kotun dai ta tabbatar da hurumin ta a kan ƙarar da ta shafi hakkin dan Adam da Aminu Babba DanAgundi, Sarkin Dawaki Babba ya shigar yana kalubalanci dokar da majalisar dokokin jihar ta yi wa Masarautar inda ya ce hakan tauye masa hakkinsa. Waɗanda suka amsa sun hada da gwamnatin jihar Kano, da majalisar dokokin jihar, da hukumomin tsaro daban-daban.
Kotun zata yanke hukuncin ne a dai dai lokacin da ake ci gaba da tabka rigingimun siyasa kan masarautar. Gwamna Abba Yusuf ya mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano bayan ya gyara dokar Masarautar da ta soke masarautun jihar biyar. Wannan matakin dai ya tsige Aminu Ado Bayero, wanda tun daga lokacin ya ƙalubalanci gyaran.
Sarakunan biyu dai na samun goyon bayan ɓangarorin siyasa masu hamayya da juna: Aminu Ado APC ke goyon baya, da kuma Sanusi Lamido da NNPP ke marawa.
Aminu Ado wanda a yanzu jami’an tsaro ke ba shi kariya, yana zaune ne a kusa da gidan gwamnati, yayin da magoya bayan Gwamna Yusuf suka mamaye fadar Sarkin domin nuna goyon bayansu ga Sanusi Lamido II.
Rikicin shari’a da dama dai na faruwa a kan masarautar, ciki har da hukuncin wata babbar kotun tarayya da ta yanke biyan Aminu Ado diyyar Naira miliyan 10 bisa zargin daurin gidan da aka yi masa.
Yayin da kotu ke yanke hukunci kan makomar sabuwar dokar masarautar, babban lauyan gwamnatin Kano, Haruna Isah Dederi ya zargi wasu bangarori da yunƙurin hukunta jihar bisa rashin adalci. Ya jaddada aniyar gwamnatin jihar na daukaka kara kan hukuncin da kotun tarayya ta yanke na diyyar, yana mai cewa ba a tauye hakkin Aminu Ado ba.