Akwai matukar zullumi, fargaba da tsoro yadda sha’anin tsaro ya yi bahaguwar tabarbarewa a Arewacin Kasar nan lamarin da ya kamata a ce tun tuni an dauki kwararan matakan shawo kan matsalar wadda ta hanawa al’umma bacci da idanu biyu, amma kullum lamarin ta’azzara yake kara yi.
Babban abin damuwa shi ne yadda masu rike da madafun iko ke nuna bambanci wajen daukar matakan lamurran tsaro tsakani Arewaci da Kudancin Kasar nan domin dukkanin wadanda ke bibiye da lamurran da ke faruwa a Nijeriya sun san cewar ko kadan Gwamnati ba ta wasa da lamari irin wannan a Kudu a yayin da a Arewa kuwa ake masa riko irin na sakainar- kashi.
A yayin da wani jami’in dan sanda ya kashe wata mata a Jihar Lagas a watan da ya gabata ai bakidaya kasar kamawa ta yi da wuta, aka yi ta Allah- wadai. To amma a ranar Talatar makon jiya a yayin da jirgin sojoji maras matuki ya yi wa Fulani 38 kisan gilla a yankin Rukubi a Doma da ke a Jihar Nasarawa kusan ba wanda ya ce uffan kamar yadda jaridar Daily Trust ta ranar Lahadi ta bayyana a sharhinta na musamman.
Kwana daya kacal kafin wannan harin, kafafen yada labarai sun ruwaito yadda sojojin sama suka kashe dimbin al’umma a Galkogo da ke a Karamar Hukumar Shiroro da ke a Jihar Neja. Shi ma lamarin kamar sauran ya faru ba tare da Hukumomi da al’umma sun nuna ko wace irin kulawa ballantana a dauki mataki ba.
Shakka babu ire- iren wadannan matsalolin na tabarbarewar sha’anin tsaro da kisan gillar da ake yi wa jama’ar da su ji ba, ba su gani ba, suna faruwa kusan a kodayaushe a Arewa. Da yawa daga ciki ma ko a kafafen yada labarai ba za a ji su ba.
A yau yadda al’amurra ke faruwa a Nijeriya tamkar rayukan wasu sun fi na wasu muhimmanci. Misali ta’addancin da aka yi a Rukubi ba shine irinsa na farko ba, hasalima ba ma shine na goma da ke a faruwa a yankin Arewa a kusa da gidaje ko gonaki ko sansanin ‘yan gudun hijira daga jami’an sojoji ba kuma duka a na fakewa da uzurin yaki da ta’addanci. Yadda ake cewar an yi kuskuren kai wasu hare- haren da walakin.
Abin da ke da ban tsoro shine Rundunar Soji da ke da alhakin hare- haren har zuwa yanzu sun zabi yin shiru ba tare da cewa uffan ba. Jama’a da dama na da ra’ayin yadda Hukumomin Tsaro ke tunanin lamarin zai wuce kawai ta rashin cewa uffan ga munanan hare- haren ya nuna yadda suka dauki rayukan wasu al’ummar kasara nan wanda kuma da zarar maganar ta wuce ta salon yin shiru sai kuma daga baya a sake irin wannan kisan gillar ba kuma daya ba, ba biyu ba.
Ko yaushe ne za a dakatar da irin wannan harin na sama ko kuma yaushe ne za a sake kai hari na gaba kuma mutane nawa ne za a kashe? Ire- iren wadannan tambayoyin ne al’ummar Arewa da ake yi wa kisan gilla ke yi a kodayaushe wadanda ke fatan ganin wadanda lamarin ya shafa sun kawo karshen wannan gagarumar matsalar.
A wata kididdiga da Daily Trust ta yi ta bayyana cewar adadin mutane 260 ne harin saman sojoji ya kashe a mabambantan lokuta 13 tun daga shekarar 2014. Binciken ya nuna biyar daga ciki sun faru ne a Borno da ke a Arewa-Maso-Gabas a inda mutum 116 suka rasa rayukan su a tsakanin watan Maris 2014 da Satumba 2021 ciki kuwa har da harin saman da aka kai a sansanin ‘yan gudun hijira na Rann a inda mutane 53 suka ce ga garin ku nan a Yuni 2017.
Ba a nan wannan kisan gillar na ba gaira ba dalili wanda ke cike da alamar ayar tambaya ya tsaya ba, domin kuwa an kai ire- iren harin na sama a Jihohin Neja da Zamfara a inda rahotanni suka nuna mutane 95 sun bakunci lahira a tsakanin 2019 da makon jiya. A Jihohin Yobe, Katsina da Nasarawa kuwa an kai harin daya- daya a inda mutane 49 suka bakunci lahira ciki har da Fulani 38 da aka kashe a ranar Talatar makon jiya.
Dukkanin wadannan hare- haren a Arewacin Nijeriya suke faruwa, wadanda ake yi wa kisan gillar ‘yan Arewa ne amma matsalar na ci- gaba da faruwa ba kakkautawa ba kuma tare da ko wane irin kwakkwaran matakin takawa matsalar burki tamkar ba rayukan ‘yan Adam ake kashewa ba.
Hare- hare irin wannan har 13 ba abu ne da za a dauka da wasa ba, lamari ne da ke bukatar binciken diddigi domin gano bakin zaren inda matsalar take. Rashin daukar matakin da ya kamata daga Shugaban Kasa shi ya kawo ci gaba da fuskantar matsalar ba tare da hana aukuwar hakan a gaba ba domin ko sau daya ba a ji an kammala bincike daya daga cikin hare-haren kisan gillar ba ko kuma aka bayyana sakamakon ga jama’a.
Abin damuwa ne yadda Shugaban Kasa ke ci gaba da yin shiru a lamarin da ya shafi rayuwa da mutuwar al’ummar kasarsa da ba su ji ba ba su gani ba duk da rantsuwar da ya yi ta kare rayukan al’umma wanda kuma wannan matakin ne Hukumomin Tsaro suka bi wanda tabbas Shugaban Kasa ne ke da babban laifi sama da na shugabannin hukumomin tsaron da ya nada.
Wajibi ne Gwamnatin Nijeriya ta sani cewar kalubalen yaki da ta’addanci tilas ne ya gudana tare da kare ‘yancin dan Adam musamman ‘yancin rayuwa. Yawaitar yadda ake yi wa al’ummar Arewa kisan kare dangi da sunan yaki da ta’addanci ya kai matakin da ba za a ci gaba da lamunta da hakan ba wanda ya zama tilas a fada da babbar murya cewar ya zama dole a takawa wannan gagarumar matsalar burki domin ba rayuwar da ta fi wata daraja.
A yayin da Gwamnati da Hukumomin tsaro suke da alhakin rashin kare rayukan ‘yan kasa musamman rayukan al’ummar Arewa da ake kashi tamkar kiyashi ya kamata su dauki muhimman matakan ganin ba a sake samun afkuwar hakan ba; ya zama tilas shugabannin Arewa su tashi tsaye tsayin daka wajen nuna muhimmancin rayukan al’ummar su tare da yin Allah- wadai ga faruwar hare- haren da uwa uba tunkarar matsalar a Gwamnatance da murya daya domin ganin ba a ci gaba da yi wa wadanda ba su san hawa ba ba su san sauka ba kisan gilla har kuma lamarin ya wuce ba tare da daukar ko wane irin mataki ba.
Gagarumar matsalar shine idan har Hukumomin tsaro za su ci gaba da daukar alhaki, ita kuwa Fadar Shugaban Kasa ta kasa daukar matakii, to ba a san ranar kawo karshen matsalar ba haka shi ma Gwamna Samuel Ortom zai ci gaba da yi ciki har da harin kwanan nan.
Kamar yadda aka sani a yanzu kusan shekaru takwas, Ortom yana amfani da karfin ofis dinsa wajen kuntatawa Fulani wadanda ‘yan kalilan ne da ba su da rinjaye a Jiharsa. A bayyane ya assasa dokoki masu tsauri da manufar karya tattalin arzikin Fulani da hana masu walawa kamar yadda ra’ayin Daily Trust ya nuna.
A kodayaushe kalaman da yake furtawa na yaki ne da tarzoma, ba wai na zaman lafiya da fahimtar juna ba kamar yadda ya kamata ya yi a matsayinsa na shugaba. Ya kirkiri jami’an tsaro na yanki tare da yunkurin ba su bindigogin AK- 47 domin cikar burinsa a kasar da kowa yake da ‘yancin zama a duk Jihar da yake bukata.
Ortom ya bayyana Fulani marasa rinjaye a matsayin “makasa’ kuma ‘yan ta’dda” da kuma mafi rinjayen jama’ar Jihar a matsayin wadanda ake kashewa duk da cewar Fulanin ne hare- haren na sojoji da ke da alamar ayar tambaya ke yi wa kisan kiyashi.
Kisan gillar na Fulani 38 jim kadan da biyan miliyan 29 na kudin tarar daya daga cikin dokokin kuntatawar da Ortom ya kirkira a Benue ya nuna yadda suke rayuwa a Jihar.
Shin sai wane lokaci ne Gwamnatin Tarayya da Majalisar Kasa za su takawa siyasar kuntatawa jama’a da Ortom ke yi? Shin sai yaushe ne shugabannin hukumomin tsaro za su ci gaba da yin shiru a yayin da jami’an su ke harba kunamar bundiga ga wadanda ba su ji ba ba su gani ba? Shin sai yaushe ne Shugaba Muhammadu Buhari zai ci gaba da rufe bakinsa duk da a na kashe dimbin al’ummarsa a karkashin mulkinsa? Shakka babu jinin wadanda aka kashe da kukan wadanda ke raye na bukatar amsa tare da dakatar da wannan danyen aikin bakidaya.