A daidai wannan lokacin da ake bikin ranar fadakarwa a kan hanyoyin kare al’umma a kan yadda mutane ke kashe kansu, ya kamata a yi amfani da wannan lokacin wajen fadakar da al’umma a kan yadda ake samun yawaitar masu kashe kansu a fadin kasar nan.
A kwanakin baya ne rahoton yadda wata sananniyar mata a Legas ta yi kokarin kashe kanta sakamakon matsalar da ta samu a da masoyinta.
Da badan masu wucewa ba, da suka hana ta fadawa cikin teku, bayan ta ajiye motarta da yanzu an samu karuwa a kididdigar wadanda suka kashe kansu ke nan a kasar.
Kafin wannan ma a watan Agusta wani mutum mai matsakaicin shekaru ya fada tekun inda aka gano gawarsa bayan ‘yan kwanaki.
Duk wani kashe kai da aka yi yana zama tashin hankali ne mai girma ga iyalan wanda ya kashe kansa da al’ummar unguwa da garinsu da kuma kasa gaba daya da kuma mutane da mutumin ya bari a baya gaba daya. Ba a ma maganar kyamar da al’amarin ke bari a baya na tsawon lokaci.
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta bayyana cewa, mutum 703,000 suka kashe kansu yayin da wasu da dama suka yi yunkurin kashe kansu a lokutta daban-daban a fadin duniya.
A Nijeriya, mutum 79 suka kashe kansu a shekarar 2022, wadanda suka hada da maza 70 da mata 9 kamar dai yadda aka ruwaito a manyan jaridun kasar nan.
Wannan kididdigar bata hada da wadanda ba a bayar da rahotonsu ba a kafafen sadarwa.
Kididdgar ta nuna cewa, Jihar Legas ke da mutane mafi yawa da suka kashe kansu inda take da mautum 12 sai Jihar Oyo da ke da mutum 10; Kano 4; Anambra 3; Edo, 3; Delta, 3; Ogun, 3; sai kuma Jihar Ribas wadda ke da mutum 3 da suka kashe kansu.
Haka kuma kididdigar ta nuna cewa, jihohin Borno, Bayelsa, Abia, Benue, Imo, Enugu, Neja, Filato, Jigawa, Kaduna, Kwara da yankin Abuja nada mutum 2 ko wannen su.
Yayin da sauran jihohin Ondo, Osun, Kebbi, Nasarawa, Gombe, Cross-Riber, Kogi, Adamawa, Ekiti, Bauchi, da Yobe keda mutum 1 kowannen su.
Lamarin kashe kai wani abu ne da yake aukuwa a sassan duniya, kashi 75 na masu kashe kansu sun fito ne daga kasashe matalauta kamar yadda aka lura a shekarar 2019.
Amma kuma abin lura a nan shi ne biniken da aka yi yana nuna abubuwan da suka faru ne kamar yadda aka bayar da rahotonsu a kafafen yada labarai wanda hakan ba yana nuna hakikanin kididdigar wadanda suka kashe kansu ba ne a Nijeriya.
A yayin da babu wani kundi a hukumance na bayanan wadanda suka kashe kansu a Nijeriya dole a dogara a rahottannin gidajen jarida da mukalaolin da aka yi a kan masu kanshe kansu.
Dokar Nijeriya ta Fanel Kot sashi na 27 bangare na 327, ta bayyana cewa, ‘Duk wani wanda ya yi kokarin kashe kansa, ya aikata laifin da ke kira da ‘Misdemeanour’ ana kuma iya masa daurin shekara 1 a gidan Yari’.
Dokar Nijeriya ta kuma haramta hada baki ko kuma boye bayanai na wanda ya yi niyyar aikata laifin kashe kansa, kamar yadda aka yi bayani a sashi na 27, yanki na 326 na dokar kasa ta Fanel Kot:
A saboda yana iya yiwuwa a samu mutane na boye labaran kashe kai ko kuma yukurin kashe kai saboda tsoron kada doka ta juyo a kan su.
Bayani ya nuna cewa, rahoton kisan kan da aka samu a yankin Kudu maso yammancin kasar nan ya kai kashi 0.27 a kan mutum 100 000 yayin da kuma a yankin Arewa ta tsakiya aka samu kashi 0.22 a kan mutum 100 ga mutum 100 000, Kudu maso gabashi kuma kashi 0.21 ga mutum 100 000, Kudu maso Kudu kuma kashi 0.19 ga mutum 100 000, Arewa maso Yammaci kuma kashi 0.07 ga mutum 100 000 yayin a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya aka samu kashi 0.04 ga mutum 100 000 a kididdgar da aka samu a shekarar 2019.
A mata, shan guba yana a matsayin kashi 64.5, rataya = 18.4, fadawa kogi kashi 6.6, sune hanyar da mata suka fi amfani da su wajen kashe kansu amma ga maza kuma rataye kai ya kai kashi 47.7, shan guba ya kai kashi 25.4 yayin fadawa cikin teku ya kai kashi 12.7.
Kyamar da ake nunawa wasu mutane da kuma matsalar kwakwalwa yake kai ga wasu kokarin kashe kansu ko kuma kashe kansu gaba daya. Bayani ya kuma nuna cewa, sau da yawa mutanen kan boye matsalar da suke fuskanta ne shi yasa ba a samun wanda zai taimaka masu ko kuma basa samun taimakon da suke bukata.
Ba a yi maganin hanyoyin kare aukuwar yunkurin kashe kai ba saboda karancin fadakarwa game da abin da ke haifar da yunkurin kashe kai ba da kuma rashin tattauna matsalar a bayyane.
A matsayinmu na gidan jarida mun damu kwarai a kan yadda wasu ke kashe kansu abin da yake neman ya zama ruwan dama-duniya musamman a tsakanin matasanmu, dattawa da kuma tsofaffinmu wadannda suke gann yin haka shi ne hanya mafi sauki ta kaucewa matsala ko damuwar da suke fuskanta.
Duk da munsan akwai matsalar cutar kwakwalwa da ke haifar da yadda wasu ke kashe kansu amma dole a duba gundummwar matsalar tattalin arziki a kan yadda wasu ke kashe kansu.
Mun kuma lura da cewa, dole kokarin kawo karshen yunkurin kashe kai ya hada da gudummwar bangarori da damna da suka hada da al’umma ita kanta, kiwon lafiya, aikin gona, kasuwanci, shari’a (Adalci), jami’an tsaro, siyasa da kuma kafafen sadarwa.
Dole a hada karfe da karfe ta yadda ya kamata a kuma fuskanci matsalar kai tsaye don maganin yadda ake samun masu kashe kansu a cikin al’umma yana kara karuwa.
Muna kuma da ra’ayin cewa, ya kamata a nemi hadin kan malaman addini da kuma fadakar da al’umma ta haka ne za a tabbatar da samun ci gaba a kokarin yaki da masu kashe kansu da kuma masu yukunrin kashe kansu.