Abubuwa biyu da suka faru a ‘yan kwanan baya a zauren Majalisar Kasa, da suka hada da mutuwar dan jarida, Alhaji Tijani Adeyemi, wakilin jaridar Tribune da kuma faduwar wakilin Jihar Kaduna a yayin da ake tantance shi a matsayin minister sun kara fito da tsanannin bukatar ‘Yan Nijeriya su dauki sha’anin kiwon lafiyarsu da matukar muhimmanci.
Rahoto ya nuna cewa, Adeyemi ya fadi ne a motar da ta dauke su zuwa majalisar kasa inda bayan kai shi asibiti aka tabbatar da mutuwarsa.
- A 2024 Ne Manoma Za Su Fara Shuka Sabon Irin Masara Na ‘TELA Maize’ —Farfesa Adamu
- An Sako Mahaifin Luiz Diaz Na Liverpool Da Aka Sace
Haka kuma rundunar ‘yansandan jihar Bayelsa ta tabbatar da mutuwar wani Mataimakin Kwamishina ‘Yansanda mai suna (ACP), Oluseye Odunmbaku, yayin da yake bacci a gidansa da ke Yenagoa, babban birnin jihar.
Wadannan na daya daga cikin mace-macen farad-daya da ake yi a kullum, abin da ya sa jami’ai a ma’aikatar lafiya suke nuna damuwarsu, ganin yadda ake samun karuwar mace-macen a Nijeriya. Rahottanin kafafen sadarwa sun nuna karuwar ‘Yan Nijeriya da ke mutuwa ko a cikin bacci ko kuma farad-daya nan take, abin da ke tayar da hankula ga hukumoni da al’umma gaba daya.
Akwai rahottanin da dama na yadda mutane ke mutuwa a yayin da suke zaune suna tattaunawa da abokansu ko kuma suna gudanar da wasu ayyukansu na yau da kullum.
Duk da cewa, mutuwa ta hanyar bugun zuciya ba wani sabon abu ba ne a Nijeriya amma yadda abin ya zama ruwan dare a halin yanzu shi ne abin damuwa.
Ana alakanta mutuwar farad-daya da tattaruwar matsalolin rashin lafiya da sukan yi katutu a jikin mutum ta yadda sukan tuke da haifar da bugun zuciya, abin da ke kai ga mutuwa a wasu lokuta. Amma masana sun bayyana cewa, wadannan matsaloli da lalurorin rashin lafiya da suka addabi mutum ba a rana daya suke shigowa ba, rashin kula da lafiya ne yake kaiwa lamarin ya yi muni, har ya kai ga mutuwar farad-daya.
Haka kuma jami’an kiwon lafiya sun bayyana cewa, cututtukan da kan kai ga mutuwar farad-daya ko kuma in mutum ya yi sa’a sai ya tsira da cutar shanyewar wani bangaren jiki wanda ba zai iya yin wasu harkokin rayuwarsa ba, suna nan tare da mutum na tsawon lokaci amma rashin kulawa ne ko mayar da hankali ga shan magani ke jefa mutum matsalar da ba a zata ba.
Ya kamata a kara fahimtar cewa, mutuwar farad-daya lamari ne da ke faruwa saboda dalilai masu yawa, wasu daga cikin dalilan sun hada da cutar zuciya, shanyewar wani bangare na jiki da sauran wasu cututtuka masu nasaba.
A shekarar 2019 kawai, cututtukan zuciya ne a kan gaba wajen kisan mutane a duniya, inda aka kiyasta mutum miliyan 17.9 suka mutu sanadiyyar su, wanda hakan ke nuna kashi 32 cikin 100 na adadin mace-macen da ake yi a fadin duniya duk shekara.
A shekarar 2020, bugun zuciya ya kashe maza fiye da 382,776 (1 daga cikin namiji 4 da suka mutu bugun zuciya ya kashe shi) ya kuma kashe mata 314,186 (1 daga cikin mata 5 da suka mutu bugun zuciya ta kashe ta, kamar yadda Cibiyar Kula da Cuttutukan da ake karewa na gwamanatin Amurka ta bayyana.
Bugun zuciya na iya kama namiji daga shekara 65 yayin da kuma mace sai ta kai shekara 72 kafin ta iya fuskantar barazanar kamuwa da cutar, kamar yadda rahoton shekara 2016 na Jami’ar Harbard ta kasar Amurka ya nuna.
Mata masu shekara 45 zuwa 65 da suka kamu da cutar zuciya suna iya mutuwa a cikin shekara daya, amma maza da suka kamu da cutar a wannan shekarun suna iya tsawon kwana fiye da matan. Haka kuma mata masu fiye da shekara 65 da suka kamu da cutar na iya mutuwa a cikin makwanni kadan fiye da mazan da suka kamu da cutar a wadannan sheakrun, kamar yadda Shashin Kula da Lafiyar Al’umma na kasar Amurka ya bayyana a rahotonsa na shekarar 2020.
A Nijeriya, masana harkokin lafiya sun ce, cututtukan zuciya ne ke da alhakin mutuwar mutum 500,000 kashi 33 cikin 100 na mace-macen da ake yi a kasar a duk shekara.
Amma kuma yana da matukar muhimmanci a fahimci cewa, duk da wannan kididdigar, ana iya rigakafin mutuwar farada-daya ta hanyoyi da dama. Wadanda suka hada da cin abnci mai gina jiki, motsa jiki domin wadannan za su iya kare aukuwar cutar shanyewar bangaren jiki. Bugu da kari, idan mutum ya ji yana fuskantar matsalolin da suka hada da daukewar numfashi, jiri, ciwon kirji ya kamata ya garzaya asibiti da gaggawa.
Wadannan shawarwarin ba sun zama makwafin ayyukan kwararrun likitoci ba ne, don haka in har mutum na da daya daga cikin matsalolin da aka zayyana, ya kamata ya garzaya don ganin likitansa, domin samun shawarwari da magungunan da suka kamata.
Cututtuka kamar hawan jini da damuwa suna cikin cututtukan da ke yi wa al’umma kisan mummuke, a kan haka ake ba mutane shawarar da su sa ido tare da lura da yawan aikin da suke dora wa kansu, su kuma lura da abubuwan da suke ci kamar sukari, gishiri, kitse, nama da madara su kuma kara cin kayan lambu.
Haka kuma ana ba mutane shawarar su daina shan sigari giya, a kuma rage kiba tare da motsa jiki a kai-a kai ba. Wadanna matakan ba wai su ne za su hana mutuwar farad-daya ba amma za su kai ga rage yawaitar mace-macen da ake samu na farad-daya a cikin al’umma, abin da yake neman zama annoba a Nijeriya.
Masana harkokin kiwon lafiya sun karfafa bukatar zuwa binciken likita daga lokaci zuwa lokaci don gano wasu alamomin cututtuka tun kafin su gawurta su kai ga illata mutum, don ta haka za a iya yin maganinsu a cikin sauki ba tare da wata matsala ba.
A matsayinmu na gidan jarida, muna sane da matsalolin tattalin arziki da na tsaron da ake fuskanta a Nijeriya, a kan haka ya zama dole mutum ya lura da lafiyarsa a daidai lokacin da yake fafutukar neman halaliyarsa.