Hukumar masana dake gabatar da gargadi game da kasuwa, karkashin ma’aikatar aikin gona da raya kauyuka ta kasar Sin, ta fitar da “rahoton hasashe kan aikin gona na kasar Sin, tsakanin shekarar 2023 zuwa ta 2032”, yayin babban taron hasashen aikin gona na kasar Sin na shekarar 2023, wanda ofishin nazarin sadarwar aikin gona ta cibiyar nazarin kimiyyar aikin gona ta kasar Sin ya shirya a jiya Alhamis 20 ga wata.
Cikin rahoton, an kiyasta cewa, adadin hatsin da kasar Sin za ta samar a shekarar bana, wato 2023, zai ci gaba da karuwa. Kaza lika rahoton ya nuna cewa, kasar Sin ta samu sakamako a bayyane, game da aikin kwaskwarima, da raya aikin gona da kauyuka na kasar a shekarar 2022 da ta gabata, inda aka sake cimma burin girbin isasshen hatsi.
Har ila yau, an kiyasta cewa, adadin hatsin da kasar za ta samu a bana zai ci gaba da karuwa, ta yadda wata kila zai kai tan miliyan 694, wanda a ciki, adadin shinkafa da masara zai daidaita, kana adadin gero zai karu kadan, yayin da adadin wake zai karu, kana karuwar amfanin gona da ake iya fitar da man girki daga gare su zai kai kaso 5.1 bisa dari a duk shekara.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, karfin samar da hatsi, da muhimman kayayyakin aikin gona na kasar Sin a shekarar 2023 zai kara karuwa, kuma kasar za ta samu sabon ci gaba, a fannin kafa tsarin samar da nau’ikan abinci iri daban daban. (Mai fassarawa: Jamila)