Bisa kididdigar da hukumar kula da harkokin fina-finai ta kasar Sin ta fitar, ya zuwa karfe 6:30 na yammacin ranar 3 ga watan Febrairun 2025, agogon Beijing, yawan kudaden da aka samu daga kallon fina-finai wato box office na sabuwar shekarar bisa kalandar gargajiyar kasar Sin ya kai yuan biliyan 8.257, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.14, wanda ya kafa sabon tarihi. Ya zuwa yanzu dai, yawan kudaden da aka samu daga kallon fina-finan kasar Sin a 2025 yana kan gaba a kasuwar fina-finan duniya da jimillar yuan biliyan 10.121, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.4 (Mai fassara: Mohammed Yahaya)