Daraktan hukumar makamashi ta kasar Sin Wang Hongzhi, ya bayyana a yayin taron ayyukan makamashi na kasar na shekarar 2026, wanda aka gudanar jiya Litinin, cewa a shekarar nan ta 2025, an hanzarta karkata zuwa amfani da makamashi mai tsafta a kasar Sin, kuma yawan makamashin da ba na kwal, da gas, da mai ba, da Sin ta yi amfani da su a 2025 din zai wuce kashi 20% bisa burin da ta tsara.
Bugu da kari, zuba jari a fannin makamashi mai tsafta yana karuwa cikin kuzari, yayin da sabbin makamashi ke samun ci gaba mai inganci, kana manyan ayyukan samar da wutar lantarki ta amfani da karfin ruwa, da makamashin nukiliya suna ci gaba da bunkasa cikin sauri. Har ila yau, sabon tsarin samar da wutar lantarkin na tafiya yadda ya kamata, kuma ana taka muhimmiyar rawa wajen amfani da makamashin kwal, da gas, da mai cikin tsafta da inganci.
Bisa bayanan da aka bayar, ana hasashen cewa, yawan wutar lantarki da sabbin na’urorin samar da wutar masu aiki da karfin iska, da hasken rana za su samar, zai kai kusan kilowatts biliyan 37, kuma yawan amfani da wadannan makamashi ya kai fiye da kashi 94%, yayin da yawan wutar lantarki da al’ummar kasar ke amfani da shi da aka samar bisa karfin iska, da hasken rana, ya kai kusan kashi 22% cikin jimillar lantarki da aka samar.
Kazalika, an gabatar da takardun shaidar samar da wutar lantarki bisa karfin makamashi mai tsafta har kusan biliyan 2.9, wadanda yawan musayarsu ya zarce miliyan 750, adadin da ya haura jimillar dukkanin cinikin da aka gudanar a wannan bangare a baya. Haka kuma, yawan wutar lantarki, da na’urorin samar da wutar lantarki masu aiki da karfin ruwa ke iya samarwa, ya wuce kilowatts miliyan 440, daga cikinsu yawan wutar lantarkin da Sin ke iya samarwa ta amfani da famfon ruwa, da tsumin ruwa ya wuce kilowatts miliyan 64. (Amina Xu)














