Sabon rahoton hukumar ƙididdiga ta kasa (NBS) ta bayyana cewa adadin marasa aikin yi ya ragu zuwa kashi 4.3 a Nijeriya, wanda ya nuna raguwar kashi 0.1 a cikin kwata na biyu na shekarar 2024, idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.
Adadin rashin aikin yi na matasa ya kasance kashi 6.5 a cikin kwatan shekarar 2024, yana nuna raguwa daga kashi 8.4 a cikin farkon kwatan 2024.
- Yadda Matatar Mai Ta Fatakwal Ta Fara Aiki
- Kasar Sin Za Ta Samar Da Ababen Hawa 100,000 Don Aikin Taksi Da Na Amfanin Kai Nan Da Shekarar 2030
Hukumar NBS ta fitar da rahoton kwata-kwata a ranar Litinin, wanda kuma ya nuna cewa rashin aikin yi a tsakanin maza ya kai kashi 3.4 da 5.1 a tsakanin mata.
A wurin zama kuma, yawan marasa aikin yi ya kai kashi 5.2 a birane da kashi 2.8 a yankunan karkara.
Alƙaluman NBS sun nuna cewa a kashi na biyu na shekarar 2024, yawan ‘yan Nijeriya marasa aikin yi ya kai kashi 9.2, ya ragu da kashi 1.4 cikin dari daga kashi 10.6 da aka samu a farkon kwatan 2024.
Rabon mazan da ba su da aikin yi ya kai kashi 7.1, yayin da mata ke fama da rashin aikin yi da kashi 11.2 na kwatan wannan shekara.
A gefe guda kuma, a cikin rubu’in shekarar 2024, adadin ma’aikata a Nijeriya ya kasance kashi 76.1 na yawan mutanen da suka yin aiki, sama da 73.1 a cikin farkon kwatan 2024.
Dangane da jinsi kuma, yawan maza masu aiki yi ya kai kashi 77.2 da 75 na mata a cikin rubu’in shekarar 2024.
A cewar NBS, sabon alƙaluman ya nuna karuwar kashi 2.9 na ma’aikata idan aka kwatanta da kashi 73.2 a cikin farkon kwatan 2024. Duk da haka, kwatankwacin shekara na nuna raguwa kadan daga kashi 77.1 a 2023 Bugu da kari, yawan masu aikin yi a cikin birane ya kasance 73.2 da 80.8 a yankunan karkara a cikin rabin shekarar 2024.
NBS ta bayyana hakan ne a cikin rahoton da ta wallafa a shafinta na yanar gizo, inda ta ce, “Wannan wani karin ci gaba ne idan aka kwatanta da kashi 69.5 da kashi 78.9 a farkon kwatan shekarar 2023.
Adadin shiga aiki a tsakanin yawan shekarun aiki ya ƙaru zuwa 79.5 a cikin kwata na biyu na shekarar 2024 daga kashi 77.3 a farkon kwatan 2024.
Aiki na yau da kullun ya kasance mai girma na kashi 93. ƙididdigar ofishin ta ce kashi 3.7 na yawan mutanen da suka yi aiki suna noma ne a cikin kashi na biyu na shekarar 2024.