Cibiyar cinikayyar waje ta kasar Sin ta bayyana a yau Litinin cewa, yawan ‘yan kasuwa na kasashen waje da suka halarci bikin baje kolin hajojin da ake shigowa da su kasar Sin, da wadanda ake fitarwa daga kasar, da aka fi sani da Canton Fair, karo na 136 a birnin Guangzhou ya kai dubu 253, wannan shi ne karo na farko da yawansu ya zarce dubu 250, wanda ya kai matsayin koli a tarihi. Manyan kamfanonin kasashen waje da suka halarci bikin ya zarce 300 wato ya kai 308 da karo na farko.
Ya zuwa ranar 3 ga wannan wata, ‘yan kasuwa dubu 253 daga kasashe da yankuna 214 sun halarci Canton Fair karo na 136, yawansu ya karu da kashi 2.8 cikin dari bisa na bikin na karon da ya gabata. A cikinsu, ‘yan kasuwa daga kasashe wadanda ke cikin shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya ya kai kashi 60 cikin dari, wato dubu 165, wanda ya karu da kashi 3.7 cikin dari. Adadin ‘yan kasuwa daga yankin Gabas ta Tsakiya ya fi yawan karuwa, wato ya kai dubu 34, wanda ya karu da kashi 32.6 cikin dari. Yawan ‘yan kasuwa daga kasashen Turai da Amurka ya kai dubu 54, wanda ya karu da kashi 8.2 cikin dari. (Zainab Zhang)