Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta gargaɗi dukkan jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar muƙamai daban-daban cewa su bi dokoki da ƙa’idojin da Dokar Zaɓe ta 2022 ta gindaya a lokacin yaƙin neman zaɓe har zuwa bayan jefa ƙuri’a.
Hukumar ta ce bin waɗannan dokokin ne za su taimaka wajen tabbatar da an samu nasarar gudanar da zaɓukan 2023 ba tare da tashe-tashen hankula ko ruɗani ba.
Kwamishinan Zaɓe na Ƙasa na Jihar Kuros Riba, Alalibo Johnson ne ya yi wannan gargaɗin ranar Alhamis a Kalaba, lokacin da ya ke jawabi ga masu ruwa da tsaki kan muhimmancin Sashe na 87 zuwa na 89 na Dokar Zaɓe ta 2022.
“Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ba za ta lamunci saɓa wa Dokar Zaɓe ta 2022 ba. Saboda haka na ke jaddada cewa a kauce wa zage-zage da munanan kalamai kan ‘yan takara a lokacin kamfen.
“Kuma kada a yi duk abin da zai haifar da tashe-tashen hankula da ɓarkewar rikici.
“Sashen Sa-ido Kan Jam’iyyu zai zaƙulo duk inda wata jam’iyya ko ɗan takara ya karya doka domin yin hukuncin da ya yi daidai da dokar da aka ƙarya.”
A jawabin sa, Johnson ya ce akwai katin shaidar zaɓe har sama da 90,000 waɗanda ba a karɓa ba a Jihar Kuros Riba.
Saboda haka ya yi kira ga jam’iyyu su zaburar da magoya bayan su cewa su hanzarta karɓar katin shaidar rajistar su kafin zaɓe a dukkan jihohin ƙasar nan.
Abubuwan Da INEC Ta Haramta Lokacin Kamfen:
A farkon Satumba ne dai INEC ta fayyace wa jam’iyyu da ‘yan takara wuraren da dokar zaɓe ta haramta yin kamfen da tarukan siyasa.
Yayin da ya rage saura kwana huɗu a fara kamfen na zaɓen shugaban ƙasa, sanatoci da na mambobin majalisar tarayya, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta gargaɗi jam’iyyu da ‘yan takara cewa su guji take dokoki, musamman dokokin da hukumar ta haramta a lokacin kamfen.
Kakakin Yaɗa Labarai na INEC, Festus Okoye ne ya bayyana haka a wancan lokacin.
Za a fara kamfen ɗin zaɓen shugaban ƙasa, sanatoci da mambonin majalisar tarayya a ranar 28 ga Satumba, yayin da za a yi zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya a ranar 25 ga Fabrairu, 2023.
Okoye ya bayyana cewa wuraren da dokar INEC ta hana yin kamfen da tarukan siyasa sun haɗa da coci-coci, masallatai, gine-gine da ofisoshin gwamnatin tarayya, na jihohi ko ƙananan hukumomi da kuma amfani da mutum-mutumin ‘masquarade’.
Ya ce ya zama wajibi jam’iyyu da ‘yan takara su bi ƙa’idojin da Dokar INEC ta 2022, Sashe na 92 ya gindaya.
Daga cikin sharuɗɗan da Okoye ya jaddada, akwai yin hani da amfani da mutum-mutumin domin ƙara wa taron siyasa armashi, yin amfani da wuraren ibada, ofisoshin gwamnati ko gine-ginen gwamnati domin yi wa ma’aikata kamfen da sauran su.
“Sashe na 92 na Dokar Zaɓe ta 2022 ya hana rubutawa ko rera taken jam’iyya ko na ɗan takara ɗauke da kalaman zagi, cin fuska ko aibata wani ɓangaren addini, yare, ƙabila ko wani yankin jama’a.
“Ba a yarda a riƙa zage-zage a lokacin kamfen ko tarukan siyasa ba. Kuma banda kalaman da ka iya harzuƙa wani ko wasu gundun jama’a su hasala har su tayar da hargitsi. A guji amfani da yare ana aibata wani yare, kuma banda shaguɓe da kalaman aibatawa da ka iya harzuƙa wasu ɗaukar doka a hannun su.
“Sashe na 3 na wannan doka ya haramta kamfen ko tarukan siyasa a wuraren ibada, ofishin ‘yan sanda, ofisoshin gwamnati da gine-ginen gwamnati. Saboda haka ba a yarda a tallata jam’iyya ko ɗan takara a waɗannan wurare ba.
“Sashe na 2(5) kuma ya haramta jam’iyya ko ɗan takara ya yi amfani da ‘yan daba ɗauke da makamai. Kada jam’iyya ko ɗan takara ya yi amfani da wasu jami’an tsaro masu zaman kan su ɗauke da makamai a wurin kamfen, taro ko wurin zaɓe.
“Sashe na 7(a) (b) da kuma Sashe na 8 sun jaddada cewa duk wanda ya karya Sashe na 92 za a yi masa tarar naira miliyan 1 ko ɗaurin shekara 1, idan ɗan takara ne.
“Idan jam’iyya ce ta karya dokar, za a yi mata tarar naira milyan 2. Idan ta ƙara kuma tarar naira miliyan 1.
“Wanda aka kama ya tayar da hargitsi ko ya yi amfani da makami kuma za a yi masa tarar naira 500,000 ko ɗaurin shekaru uku, ko kuma a haɗa masa duka biyun,” inji Okoye.