“Mutane a fadin duniya suna fatan samun zaman lafiya, mutunci da wadata a nan gaba.”Wannan shi ne kiran da Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yi a taron koli dangane da makomar dan Adam da ya gudana a Majalisar a kwanan baya.
A matsayinta na mamba ta dindindin a kwamitin sulhu na MDD, kasar Sin ta ba da cikakken goyon baya ga wannan taro. Inda wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya jaddada a wajen taron cewa, dole ne dukkan bangarorin duniya su girmama, da kare tsarin kasa da kasa da ya kasance a karkashin jagorancin MDD, da kiyaye hakki da moriyar kasashe masu tasowa, da inganta dunkulewar tattalin arzikin duniya, don tabbatar da moriyar dukkan bangarori, da dai sauransu.
- Sin Ta Kira Taron Nazarin Yanayi Da Aikin Raya Tattalin Arzikin KasarÂ
- Kasar Sin Ta Harba Taurarin Dan Adam 5 Zuwa Falakinsu
“Samun ci gaba mai dorewa, da kaucewa barin wani a baya, shi ne, kuma zai kasance a ko da yaushe babban makasudin ra’ayi na wanzuwar bangarori masu fada a ji daban-daban.” Wannan magana na cikin yarjejeniyar da aka zartas a wajen taron kolin na wannan karo. Hakan ya nuna wata alamar samun makomar duniya mai haske.
Matukar dukkan bangarorin duniya sun yi kokarin aiwatar da yarjejeniyar, kuma sun maye gurbin taho-mu-gama da hadin gwiwa, da kokarin hakuri da juna maimakon mai da wani bangare saniyar ware, to yunkurin tabbatar da makomar duniya mai haske ba zai zama mafarki ba. (Bello Wang)