Wani mai rajin kafa kasar Yarbawa, Cif Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya mika koke ga firaministan kasar Birtaniya, Keir Starmer.
Duk da cewa, ba a san meke kunshe cikin takardar koke-koken ba, amma ana ganin ba zai rasa nasaba da kafa kasar ‘yan kabilar Yarbawa da mafi yawancin su ke zaune a yankin Kudu-maso-Yammacin Nijeriya ba.
- Arafat: NAHCON Ta Jagoranci Yi Wa Kasa Addu’a
- Al’ummar Arewa: Bango Ne Ya Tsage Kadangare Ya Samu Wurin Shiga
Wata majiya mai tushe, ta tabbatar da cewa, Igboho ne ya gabatar da takardar koken a ofishin Firaministan Birtaniya da ke birnin Landan a madadin shugaban kungiyar Yarbawa ta kasa kuma fitaccen masanin tarihi, Farfesa Banji Akintoye.
A cewar majiyar, gabatar da koken na da nufin samun goyon bayan firaministan da kuma gwamnatin Birtaniya, wacce tsohuwar uwargida ce ga Nijeriya a lokacin mulkin mallaka, kan samar da kasar Yarbawa mai cin gashin kanta daga Nijeriya.
Daga cikin jiga-jigan da suka raka Igboho domin mika koken sun hada da shugaban matasan kungiyar na kasashen waje, Annabi Ologunoluwa; Mataimakin shugaban Ifeladun Apapo, Fatai Ogunribido; Babbar Sakatariyar Yada Labarai ta kungiyar Yarbawa, Alhaja Adeyeye, da mamban kungiyar Yarbawa ta kasa, Paul Odebiyi.