Kotu ta yi watsi da karar da Umar Abdullahi Ganduje, na jam’iyyar APC ya shigar agabanta na kalubalantar nasarar Tijjani Abdulkadir Jobe na NNPP a zaben majalisar wakilai ta tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Maris. 2023.
Alkalin kotun, ya yi watsi da karar sabida rashin cancantarta.
Kotun ta bayyana cewa, mai shigar da kara ya kasa gabatar da isassun shaidu da za su tabbatar da zargin da ya yi a yayin gudanar da zaben.
Kotun ta ci tarar mai shigar da karar Naira N200,000.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp