A wani yunƙuri na tabbatar da baƙi daga maƙwabta ba su yi katsalandan a zaɓen Nijeriya na 2023 ba, Hukumar shige da fice ta ƙasa (NIS) ta ƙwace katunan zaɓe da katin ɗan ƙasa daga hannun baƙin waje guda 6,216 a iyakokin ƙasar guda 21.
Shugaban hukumar ta NIS, CGI Isa Idris Jere ya nuna wa manema labarai katin ɗan ƙasa 3,823 da katin zaɓe 2,393 wanda aka ƙwace daga hannun baki a wasu iyakokin ƙasar nan da suka haɗa da jihohin Nasarawa, Kebbi, Sakwato, Adamawa, Akwa Ibom, Kogi, Yobe, Kwara, Taraba, Filato, Legas, Ogun, Oyo, Zamfara, Jigawa, Edo, Bauchi da Neja da sauran guda uku.
Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba lokacin da hukumar ta yi ganawar gaggawa da manyan jami’anta da suka haɗa da kodinetoci na rassa da kwamandojinta da ke faɗin Nijeriya a shalkwatanr hukumar a Abuja, kan shirye-shiryen da hukumar za ta gudanar lokacin zaɓe.
CGI Jere ya ja kunnen jami’ansa kan su ɗauki ranakun 25 ga watan Fabrairu da 11 ga watan Maris na 2023, a matsayin wata dama ta nuna ƙwarewarsu wajen kula da iyakokin ƙasa da tattara bayanan sirri.
Ya gargaɗe su da cewa duk wani jami’i da aka samu yana haɗa kai domin cin amanar ƙasa za a ɗauke shi a matsayin mai zagon ƙasa kuma zai fuskanci fushin hukumar.
Shugaban hukumar ya yi gargaɗin cewa tsauraran matakai na jiran duk wani baƙo da ya yi yunƙurin shiga harkokin zaɓen ƙasar nan. Inda ya yi ƙarin hasken cewa, tun daga lokacin da aka kama waɗannan baki an mayar da su ƙasashensu ne bisa bin dokar Ƙungiyar Bunƙasa Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) kan ‘yancin tafiye-tafiye.
A cewarsa, dokar zaɓe ta 2022 da kuma kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima sun ɗora nauyi a kan masu ruwa da tsaki a harkokin zaɓe, musamman ma hukumar NIS, “wannan ne ya sa muka yanke shawarar ɗora wa kwanturololinmu alhakin duk wata gazawa da jami’ansu suka nuna.”
CGI Jere ya nanata aniyar gwamnati ta tabbatar da sahihin zaɓe na gaskiya da adalci, sannan ya buƙaci manyan jami’an hukumar da su ƙara ƙaimi a dukkan iyakokin ƙasar nan lokacin gudanar da ayyukansu domin tabbatar da samun nasarar zaɓe.
Ya jaddada wajibcin nuna ɗa’a daga jami’ai da kuma jajircewa wajen ci gaba da sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.
Ya ce, “A matsayinmu na jami’an gwamnati, an haramta mana nuna ɓangaranci a lokacin zaɓe da kuma bayan zaɓe. Domin haka, hukumar tana amfani da wannan damar wajen wayar da kan dukkan ma’aikata ta hannun kwanturololin bisa buƙatar su ci gaba da kasancewa ‘yan babu ruwanmu gabanin zaɓe da lokacin zaɓe da kuma bayan zaɓe.
“Idan ba mu manta ba cewa rattaba hannu kan dokar zaɓe ta 2022 da shugaban ƙasa ya yi a bara, ya sa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta fitar da jadawalin lokacin zaɓe, inda ta tsayar da zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya a ranar 25 ga Fabrairu, 2023, sannan zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun jiha zai biyo baya a ranar 11 ga Maris, 2023.
“Dukkanmu muna sane da irin muhimmancin da gwamnatin tarayya ta bai wa Zaɓen 2023 wanda zai kawo ƙarshen mulkin shekaru 8 na gwamnatin da ke ci yanzu, sannan kuma ƙara cika shekaru 24 da dawowar mulkin dimokuraɗiyya a ƙasarmu mai albarka,” in ji shugaban NIS.
Ya kuma yi gargaɗin cewa duk wani mai zagon ƙasa ko rashin ɗa’a gabanin zaɓe da da lokacin zaɓen da kuma bayan zaɓen zai fuskanci hukunci mai tsanani.
Ya umurci manyan jami’an shige da ficen na ƙananan hukumomi 774 da ke faɗin ƙasar nan da su zurfafa sa ido cikin sirri kan hulɗa da bakin ‘yan ƙasashen waje a dukkan yankunansu domin tabbatar da cewa babu wani baƙo da ya shiga cikin harkokin zaɓen Nijeriya.