Tsohon Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya bayyana aniyarsa na tsayawa takarar gwamnan Jihar Kebbi a zaɓen 2027.
Malami ya tabbatar da hakan ne yayin wata hira da kafar DCL Hausa a ranar Litinin, inda ya ce yana da tabbacin samun goyon bayan jama’a.
- ’Yansanda Sun Tura Tawaga Don Ceto Ɗaliban Da Aka Sace A Kebbi
- An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing
“Dokokin INEC ba su ba mu damar fara yaƙin neman zaɓe ba tukuna, amma idan lokacin ya yi, za ku ga cewa muna da goyon bayan al’ummar Jihar Kebbi,” in ji shi.
“Na yadda na tsaya takara, kuma babu gudu ko ja da baya. Insha Allah, za mu yi nasara saboda muna da mutane da suka yadda da mu.”
Ya kuma soki gwamnatin APC ta yanzu, inda ya ce manufofinta sun janyo koma baya a tattalin arziƙi, rashin tsaro, da rufe masana’antar shinkafa da ke aiki shekaru da dama a Arewa.
Ya ƙara da cewa rashin tsaro ya tilasta wa manoma da dama barin gonakinsu.
Malami ya ce dalilin tsayawarsa takara shi ne domin magance rashin tsaro, farfaɗo da noma, da kare haƙƙoƙin mazauna Kebbi.
A farkon wannan shekara ne, ya koma ADC kuma yana aiki tare da ‘yan adawa domin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu.














