An bayyana dan takara a karkashin jam’iyyar APC, Misa Musa Jauro a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike gurbi a mazaɓar Ganye ta jihar Adamawa da aka gudanar ranar Asabar.
Jauro ya samu kuri’u 16,923 inda ya doke abokin takararsa na jam’iyyar PDP, Buba Muhammad Joda wanda ya samu kuri’u 16,794.
- Na Hadu Da Azzalumai Da Mayaudara Farkon Shigata Kannywood – Dan’duniya
- Me Ya Sa Ciwon ACL Ya Zama Barazana Ga ‘Yan Wasan Kwallo?
Baturen zabe na hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Tukur Ahmed ne ya bayyana sakamakon zaɓen da sanyin safiyar Lahadi.
An gudanar da zaɓen ne domin cike gurbi a majalisar dokokin jihar.
An samar da wannan kujerar ne a watan Mayun shekarar da ta gabata lokacin da dan majalisar wakilai Abdulmalik Musa ya rasu.
Marigayin dan jam’iyyar APC ne tun asali.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp