Jam’iyyar NNPP a jihar Katsina ta yi zargin yin amfani da kuɗi na fitar hankali wajan sayen kuri’un Daliget a zaɓen fidda gwani na fitar da dan takarar gwamnan APC da ya gabata.
Shugaban Jam’iyyar NNPP reshe Jihar Katsina, Hon. Sani Liti, ya bayyana haka a lokacin taron manema labarai da aka yi a Katsina.
Hon. Sani Liti ya ƙara da cewa kimanin naira na gugar naira biliyan biyu da miliyan ɗari bakwai da hamsin aka yi amfani da su wajan sayen kuri’un Daliget 1,805 a cikin rana ɗaya kawai.
“Idan har gwamnatin bata ɗauki mataki akan wannan al’amari ba, to ba’a san inda wannan ƙasa zata faɗa ba a sakamakon muzanta darajar naira da gwamnati ta taimaka aka yi a Nijeriya” in ji shi
Sannan ya ƙara da cewa suna da duk wani bayani na iri kuɗaɗen da aka kashe wajan zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC wanda mutum tara suka tsaya takara. Sai dai ya ce cikekken bayani na nan tafe nan gaba.
Haka kuma jam’iyyar NNPP ta yi koken cewa gwamnan babban bankin Nijeriya, Mista Godwin Emefele, ya faɗa siyasa wanda hakan ya ci karo da dokar ƙasa, ya ce ya kamata ya sauka daga aikinsa tun kafin lokaci ya kure masa.
Hon. Sani Liti ya ce ta inda za a tabbatar da wannan ikirari nasu shi ne, yadda shugaban baban bankin Nijeriya ya yi amfani da kuɗi naira miliyan 100 wajan fom ɗin takarar shugaban ƙasa a kakar zaɓen da ake ciki.
Jam’iyyar NNPP ta ce baya ga sayen fom da shugaban baban bankin Nijeriya ya yi, ya kuma sayi motoci 100 da zai yi amfani da su wajan yakin neman zaɓe kafin ya janye takararsa.
Hon. Sani Liti ya ce kasancewar, Godwin Emefele, ɗan wata jam’iyyar kawai ya haramta masa ci gaba da zama gwamnan baban bankin Nijeriya, ya ce idan kuma hakan bata samu ba, shugaban ƙasa da kansa ya kamata ya nuna halin girma da mutunci wajan sauke shi daga kujerarsa.
Kazalika jam’iyyar NNPP ta yi zargin cewa, Godwin Emefele, yana da hannu dumu-dumu wajan faɗuwar darajar naira a Nijeriya wanda ke neman kassara kasar ta fuskar tattalin arziki.