Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya tabbatar da cewa shekarar 2025 za ta zama shekarar da za a ƙarfafa gyare-gyaren da ake aiwatarwa ƙarƙashin Ajandar Sabunta Fata ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, waɗanda tuni suke haifar da sakamako mai kyau a fannonin tsarin tattalin arziki.
Idris ya bayyana haka ne a ranar Talata a Abuja a wurin taron atisayen shugabanci da gudanarwa wanda gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON) ya shirya wa ma’aikatan sa.
- Kano Ta Nemi Gwamnatin Tarayya Ta Miƙo Mata Rabonta Na Tsawon Shekaru 25 Daga Shirin NLNG
- Ministan Harkokin Wajen Sin Wang Yi Ya Lashi Takobin Zamowar Kasar Sin Ginshikin Zaman Lafiya Da Hadaka
A jawabin sa, Idris ya jaddada rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen bayyana nasarorin gwamnatin.
Ya ce: “Babu tantama, ina tabbatar maku da cewa shekarar 2025 za ta ƙarfafa gyare-gyaren Ajandar Sabunta Fata ta Shugaban Ƙasa, waɗanda tuni suke haifar da sakamako mai kyau a fannoni daban-daban na rayuwar mu ta zamantakewa, tattalin arziki, da siyasa.”
Ministan ya jaddada shirin Shugaba Tinubu na aiwatar da manyan gyare-gyaren kuɗi don ƙara wa jihohi da ƙananan hukumomi yawan kuɗaɗen da suke samu domin ciyar da al’ummar Nijeriya gaba, bisa tsarin gaskiya na tarayya.
Ya yi kira ga VON, a matsayin sa na gidan watsa labaran ƙasa da ƙasa, da ya bayyana wa da duniya nasarorin da Nijeriya take samu.
Ya ce, “Dole ne gidan rediyon Muryar Nijeriya ya sanar wa da duniya cewa Nijeriya ta dawo kan turbar aiki; cewa muna samun nasara a yaƙin da muke yi da ta’addanci, ’yan fashi, da rikicin ƙabilanci; cewa muna ƙarfafa al’ummar mu domin samar da cigaba mai ɗorewa; cewa matasan mu sun samu hanya mafi sauƙi don ilimi mai inganci ta hanyar Asusun Ba da Lamuni na Ilimi na Ƙasa (NEL), sannan kuma abu mafi muhimmanci, cewa ƙasar mu tana kan matakin sauyin makamashi wanda zai tabbatar da wutar lantarki da iskar gas mai ɗorewa don amfani a gidaje da masana’antu.”
Ya ƙara da cewa dole ne VON ta tabbatar “ba a bar giɓi ba wajen tattara nasarorin da Nijeriya take samu” ta hanyar rahotanni da nazari da ake watsa wa al’ummar duniya.
Idris ya nanata cewa gwamnati za ta ci gaba da amfani da damar da VON take da ita domin yaƙar barazanar labaran ƙarya waɗanda ke barazana ga ƙasar nan a matakin duniya.
Ministan ya yi kira ga ƙungiyoyin kafofin watsa labarai kamar VON da su rungumi fasahohin zamani domin su ci gaba da yin gogayya a duniyar watsa labarai, tare da inganta inganci da isar da shirye-shiryen su.
Ya kuma yaba wa Darakta-Janar na VON, Malam Jibrin Baba Ndace, tare da masu gudanarwa da ma’aikatan VON bisa sadaukarwar su da hangen nesa wajen tafiyar da hukumar zuwa ga kyakkyawan aiki.