Hukumomin da ke kula da wasannin kwallon kafa a kasar Ingila sun fara shirin fara amfani da fasahar tantance satar gida a karon farko a gasar cin kofin FA ta Ingila. A ranar Alhamis hukumar kwallon kafa ta Ingila ta sanar da cewa za a yi amfani da fasahar a wasanni bakwai da za a fafata a filayen kungiyoyin gasar Premier kuma hukumar FA ta ce nan gaba za a yi amfani da fasahar a wasannin gasar Premier.
Tun da farko kungiyoyin Premier sun amince da a soma amfani da fasahar a kakar wasa ta 2024 zuwa 25 amma aka jinkirta domin kammala gwaji kuma a kakar wasa ta 2022 zuwa 2023 ne hukumar kwallon Turai ta UEFA ta soma amfani da fasahar a wasannin gasar zakarun Turai. Hukumar FA ta ce fasahar za ta taimaka wajen tabbatar da tantance satar gida ta hanyar samar da hoto.
- Yadda Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa Ta Gudanar Da Tantance Sabbin Kwamishinoni
- Amurka Ba Za Ta Cimma Burinta Bisa Matakin Kara Harajin Kwastam Kan Ma’adanan Karfe Da Goran Ruwa Ba
Kuma a cewar hukumar, fasahar ba za ta ci karo da alkalanci ba amma za ta kara tabbatar da saurin tantance satar gida a wasanni sannan za a kuma yi amfani da fasahar bidiyo da ke taimaka wa alkalin wasa a wasanni takwas na gasar FA. A ranar Asabar 1 ga Maris ne za a buga wasannin FA zagaye na biyar wanda idan an kammala gasar wannan shekarar sabuwar fasahar za ta fara aiki nan take.