Jimilar ‘yan wasa 7,824 daga tawagogi 34 ne suka yi registar shiga gasar wasannin ta nakasassu ta kasar Sin karo na 12 da gasar wasanni ta Olympics ta masu bukata ta musammam karo na 9. An tsara gasar za ta fara daga gobe Talata, inda za su gudana a fadin yankunan Guangdong da Hong Kong da Macao.
Wannan ne karo na farko da za a karbi bakuncin gasannin biyu a yankunan Guangdong da Hong Kong da Macao. Gasannin sun kunshi shirye-shirye 1,876 a bangarorin wasanni 46. Inda aka riga aka kammala gasa a wasannin 6 na lokacin hunturu. (Mai fassara: FMM)
ADVERTISEMENT














