Sarkin Noman karamar hukumar Bassa da ke Jihar Filato Alhaji Ya’u Bala Jingir, ya yi kira ga gwamnatin tarayya cewa kada ta hana shigo da takin zamani daga kasashen waje.
Jingir ya ce, wannan kira ya zama wajibi, saboda rade-radin da ake yi cewa, kamfanonin yin takin zamani na Nijeriya suna ta kokarin ganin gwamnati ta hana shigo da taki daga kasashen waje.
- 2023: Atiku Ya Sha Alwashin Ƙara Wa Jihohi Da Ƙananan Hukumomi Ƙarfin Iko
- ’Yar Kasuwa Elizabeth Homes: Labarin Tashe Da Rushewarta (I)
Alhaji Ya’u Bala kuma shi ne Garkuwar al’ummar Hausawa da Fulani na yankin Pengana ya sanar da hakan ne a hirasa da manema labarai a jihar.
Ya bayyana cewa, hana shigo da taki daga waje za ta jawo babbar matsala ga manoman Nijeriya, inda ya kara da cewa, domin kamfanonin takin da muke da su, ba za su iya wadata manoman da taki ba.
Saboda haka sai ya ce, ba sa yin taki ingantatce, suna hada abubuwan da suka ga dama ne kawai a takin da suke yi, inda ya sanar da cewa, don haka bai kamata gwamnati ta hana shigo da taki daga waje ba.
Jingir ya ce, takin da ake shigowa da shi daga waje ne kawai yake da inganci, inda ya sanar da cewa, kamfanonin taki na Nijeriya ne suke son a hana shigo da taki daga waje.
A cewarsa, bayan takin da suke yi ba shi da kyau, babu shakka idan aka dogara da takin da ake yi a Nijeriya, noma ba zai inganta ba.
Sannan kuma ya yi kira ga gwamnati ta samar da taraktocin noma da takin zamani ga manoma, inda ya bayyana cewa, ta kuma ta sayi amfanin gona daga hannun manoma ta ajiye don bacin-rana da rage wa manoma asara, domin yin haka zai dada bunkasa harkokin noma a fadin kasar nan.