Da safiyar yau Laraba, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai. Yayin taron, mai ba da taimako ga ministan kasuwanci na kasar Sin Tang Wenhong, da mataimakin gwamnan lardin Hunan Wang Junshou, sun gabatar da batutuwa masu nasaba da baje kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afirka karo na 4 da za a shirya a birnin Changsha, tare da amsa tambayoyin manema labarai.
Bisa gabatarwar da Mr. Tang Wenhong ya yi, za a gudanar da baje kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afirka karo na 4 daga ranar 12 zuwa 15 ga watan Yuni a birnin Changsha dake lardin Hunan, kuma jigonsa shi ne “Sin da kasashen Afirka suna himmatuwa wajen cimma zamanantarwa”, taron da gwamnatin lardin Hunan da ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin za su dauki nauyin shiryawa tare. Taron daya ne daga cikin muhimman ayyukan mu’amalar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afirka a bana.
- Sara Da Sassaka Ba Ya Hana Gamji Toho
- ‘Yan Ta’adda Na Amfani Da Sojoji Da ‘Yan Siyasa Wajen Samun Bayanan Sirri – Zulum
A cikin ’yan shekarun nan, bisa manyan tsare-tsare na shugabannin kasashen Sin da Afirka, hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka ya samu sabon ci gaba. Musamman a gun taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da aka yi a birnin Beijing a watan Satumban bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana matakai a aikace na “Ayyuka guda 10”, a fannin hadin gwiwa tare da kasashen Afirka, wadanda suka sa kaimi ga hadin gwiwar Sin da Afirka.
A shekarar 2024, adadin ciniki tsakanin Sin da Afirka ya kai dalar Amurka biliyan 295.6, wanda ya karu da kashi 4.8 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokaci na shekarar 2023, wanda hakan ya kafa sabon tarihi a shekara ta hudu a jere.
Kasar Sin ta kasance abokiyar cinikayya mafi girma ta kasashen Afirka cikin tsawon shekaru 16 a jere. Daga cikinsu, darajar kayayyakin da kasar Sin ta shigo da su daga Afirka sun kai dalar Amurka biliyan 116.8, adadin da ya karu da kashi 6.9 bisa dari, sannan kayayyakin da take fitarwa zuwa Afirka ya kai darajar dalar Amurka biliyan 178.8, wanda ya karu da kashi 3.5 bisa dari. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp