A jajibirin bikin cika shekaru 80 da samun nasarar babban yakin ceton kasa a kasar Rasha, rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, tare da hukumar kula da harkokin fina-finai ta kasar Sin, za su gudanar da bikin tallata fim din “Red Silk” wanda Sinawa da ‘yan Rasha suka shirya a birnin Moscow. A wannan lokacin, mashirya fim din Sinawa da ‘yan Rasha, za su yi musayar ra’ayoyinsu kan yadda suka shirya fim din, tare da sanar da cewa, za a fitar da fim din a kasar Sin a watan Satumba na wannan shekara a lokacin da kasar Sin ke bikin cika shekaru 80 da samun nasarar yakin juriya na jama’ar kasar Sin kan zaluncin Jafanawa da yakin adawa da Fasistanci na duniya.
A matsayin sabon hadin gwiwa tsakanin Sin da Rasha a masana’antar fina-finai, fim din “Red Silk’ wanda aka yi hadin gwiwar shiryawa, an fitar da shi Rasha a ranar 20 ga Fabrairun wannan shekara. Kana an tsara fim din ne bisa abubuwan tarihi da suka faru a zahiri, kuma ya ba da labarin yadda ‘yan juyin juya hali na Sin da Tarayyar Soviet suka yi yaki kafada da kafada a shekarar 1927, inda suka yi nasarar raka muhimman takardu na sirri lami lafiya. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp