Kwamitin tsare-tsaren jana’izar Jiang Zemin, ya fitar da sanarwa da ke cewa, za a gudanar da taron tunawa da marigayin a ranar Talata 6 ga watan nan, a babban dakin taruwar jama’a dake birnin Beijing.
Da yammacin Alhamis din nan ne kuma, jirgin sama na musamman ya dauko gawar Jiang Zemin daga birnin Shanghai zuwa Beijing. Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping, da wasu manyan jagororin JKS, da kusoshin gwamnati, suka isa filin jirgin sama domin tarbar gawar marigayin.
Bisa wani labari daban da aka bayar, an ce, a jiya ne, mambobin kwamitin sulhun MDD suka yi shiru na minti daya, domin tunawa da tsohon shugaban kasar Sin Jiang Zemin.
A yayin fara taron na jiya ne, zaunannen wakilin kasar Ghana a MDD Harold Agyeman, kana shugaban karba-karba na majalisar na watan Nuwamba, ya bayyana juyayinsu ga gwamnatin kasar Sin da al’ummar Sinawa game da rasuwar Jiang a madadin ‘yan majalisar.
A madadin kwamitin sulhu, Agyeman ya bukaci dukkan wadanda suka halarci zauren majalisar, da su tsaya shiru na minti guda, domin tunawa da Jiang, wanda ya rasu jiya Laraba a birnin Shanghai yana da shekaru 96 a duniya. (Saminu Hassa, Ibrahim Yaya)