Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa, tana shirye-shiryen haramta wa ‘yan kasar waje sayen amfanin gona kai-tsaye a gonanakin manoman kasar nan.
Ministan Ma’aikatar Cinikayya da zuba jari Otumba Adeniyi Adebayo ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kaddamar da wani kwamitin hadda a tsakanin hukumomin gwamnatin tarayya a babban birnin tarayyar Abuja.
Ya ci gaba da cewa, tuni aka amince da wannan matakin a taron Majalisar kasa.
Adeniyi ya ci gaba da cewa, gwamnatin tarayya ta fara shirin wanzar da tsarin noma don kiwo, wanda ya kara da cewa, wannan kokarin na daga cikin kokarin da gwamnatin tarayya ke yi domin ta samar da kyakywan yanayi ga masu bukatar sayen amfanin gona.
Ministan ya kara da cewa, gwamnatin tarayya ta yi hakan ne domin ta magance kalubalen da ake samu na bunkasa fannin aikin noma a Nijeriya da kara habaka fannin aikin tattalin arzikin Nijeriya da dakile yadda ake tauye manoman wajen samun ribar amfanin gona da ya kamata su samu wajen sayen kayan amfanin.
“Gwamnatin tarayya ta fara shirin wanzar da tsarin noma don kiwo, inda ya kara da cewa, wannan kokarin na daga cikin kokarin da gwamnatin tarayya ke yi domin ta samar da kyakywan yanayi ga masu bukatar sayen amfanin gona”.
Adeniyi ya kuma koka kan yadda ‘yan kasar wajen ke cutar da manoman kasar nan wajen sayen amfanin gonakan su kai tsaye daga gonakan su ba cikin farashi mai sauki.
Ya ce, hakan ya janyo masana’antun kasar samun wadataccen amfanin gona da suke sarrafa wa zuwa sauran nau’ukan abinci saboda yadda ‘yan kasar wajen ke saye amfanin gonakan na manoman.
A cewar Ministan wannan lamarin bai dace ba domin hakan domin ‘yan kasar wajen, na sayen amfanin gonakan da manoman suka noma ne a cikin rahusa, inda kuma hakan ke janyo samar da wadataccen amfanin gona ga ‘yan kasar da kuma kara haifar da rashin aikin yi.
“Lamarin bai dace ba domin hakan domin ‘yan kasar wajen, na sayen amfanin gonakan da manoman suka noma ne a cikin rahusa, inda kuma hakan ke janyo samar da wadataccen amfanin gona ga ‘yan kasar da kuma kara haifar da rashin aikin yi”.
A na sa jawabin shugaban kwamitin Suleman Audu, ya sanar da yunkurin kwamtin wajen samar da shugabanci na gari domin a wanzar da nauyin da aka dora wa kwamitin don yin aikinsa yadda ya kamata.
Audu ya kuma yi alkawarin cewa, kwamitin ba zai baiwa Gwamnati kunya , kan aikin da aka dora masa ba.