Mai martaba Sarkin Zazzau kuma babban mataimaki na kungiyar ‘yan kasuwa, masana’antu, ma’adinai da noma ta Jihar Kaduna (KADCCIMA), Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya yi kira ga yankin Arewa da su tashi tsaye domin magance matsananciyar yunwa da za a iya fuskanta.
Da yake jawabi a wajen bikin karramawa na KADCCIMA karo na 3 da aka gudanar a Kaduna, Sarkin ya ce yankin ba ya bukatar boka da zai shaida musu cewa matsalar yunwa na tafe kuma ya kamata a farka domin noma shi ne ginshikin tattalin arziki.
- An Ɗaure Mutum 14 Kan Yaɗa Bidiyon Maɗigo A Jamhuriyar Nijar
- A Real Madrid Zan Yi Ritaya Daga Buga Kwallo, Cewar Benzema
A cewarsa, “Batun matsalar yunwa a shekara mai zuwa, ba ka bukatar boka ya gaya maka abin da zai faru, amma muna addu’a ga Ubangiji Madaukakin Sarki kuma wannan kira ne da ya kamata mutane su yi amfani da wasu hanyoyin da za su bi domin samun mafita, tabbas za ku fuskanci abubuwa wadanda ba a yi tsammani ba.
“Ya kamata mu farka daga barcin da muke yi, mu yi abin da za mu iya yi domin ginshikin tattalin arzikinmu ni a ganina shi ne noma, musamman a yankin Arewa, noma ya samu mummunar illa a bana saboda wasu guda biyu, daya ambaliya, na biyu kuma ‘yan bindiga wanda duk abin takaici ne, a yankinmu wanda ke da hadari.”
Ya taya wadanda aka karrama murna, inda ya ce sun bayar da gudunmawa sosai ga tattalin arzikin kasar nan a fannonin rayuwa daban-daban musamman a yankin Arewa.
Daga nan sai ya bayyana cewa makarantun gaba da sakandare a duniya ba kyauta ba ne inda ya ce, “Idan ‘yan Nijeriya suna son ilimi mai inganci, sai sun biya, ba wai ina cewa mutane su biye tsadar rayuwa ba saboda wasu kudaden rajistar da muke biya a makarantarmu ta Nijeriya idan har za a biya su, ka kwatanta shi da makarantun da ke ketare, za ka gano cewa muna biyan kudi kadan, idan aka kwatanta da Nijeriya”.
Shi ma da yake jawabi, Gwamna Nasir El-Rufai wanda ya samu wakilcin babban sakataren ma’aikatar kirkire-kirkire ta kasuwanci, Dakta Yusuf Saleh, ya ce a cikin shekaru bakwai da suka gabata gwamnatin Jihar Kaduna ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin ta zuba jari a sassa daban-daban na fannin tattalin arziki. .
Ya ce ma’aikatar kirkire-kirkire ta kasuwanci na bunkasa fasahar matasa don dacewa da al’amuran rayuwa daban-daban.
Shugaban masana’antun Falke, Alhaji Samaila Maigoro, ya bukaci gwamnati da ta zakulo sana’o’in da ake da su tare da karfafa musu gwiwa su kara himmatuwa ta hanyar kayayyakin aiki, horarwa da sauransu.
Shugaban KADCCIMA, Alhaji Sulieman Aliyu, ya ce kungiyar za ta bullo da wani shiri na ba da shawara ga shugabannin ‘yan kasuwa a yankin nan gaba.