Kotun Shari’ar Musulunci da ke karamar hukumar Ningi a Jihar Bauchi, ta kama wasu mutum uku da laifin aikata Luwadi don haka ta yanke musu hukuncin kisa ta hanyar jefewa da duwatsu.
Idan za a iya tunawa dai an fara shi ne a ranar 14/6/2022 yayin da dakarun HISBAH ke sintiri a karamar hukumar Ningi karkashin jagorancin Adamu Dan Kafi, inda suka gurfanar da mutane ukun bisa zarginsu da aikata Luwadi.
- Ka Yi Murabus Yanzu Ko Mu Tsige Ka – ‘Yan Majalisa Ga Kakakin Majalisar Bauchi
- An Kaddamar Da Alkur’ani Da Aka Fassara Zuwa Harshen Igbo A Abuja
Majiyarmu daga kotun shari’ar ta bayyana sunayen wadanda ake zargin da wannan laifin masu suna Abdullahi Abubakar Beti, Kamilu Ya’u da Malam Haruna wadanda kotun shari’ar ta kama da laifin yin Luwadin tare da yanke musu hukuncin.
Dakarun HISBAH din sun shaida wa kotun cewa mutum ukun an kamasu ne su na aikata Luwadi a kauyen Gwada da ke karamar hukumar Ningi.
Bayan da ya saurari dukkanin bayani kan karar, alkalin kotun, Munka’ilu Sabo Ningi, ya ware ranar Laraba 29/6/2022 domin yanke hukunci.
Da ya ke yanke hukuncin, alkalin kotun ya ce bisa dogaro da shaidun da suka bayyana a gaban kotun, kotun ta samu mutum ukun da zargin aikata Luwadi don haka ne alkali Munka’ilu Sabo Ningi, ya zartar musu da hukuncin kisa ta hanyar jefewa.
Wadanda za su bakunci lahira ta hanyar jefewa sun kunshi matasa biyu da dattijo guda daya masu suna Abdullahi Abubakar Beti dan shekara 30 a duniya, Kamilu Ya’u 20 da kuma Malam Haruna mai shekara 70 a duniya da aka yanke musu hukuncin bisa dogaro da sashin 134 na dokar jihar Bauchi na shekarar 2001 gami da dogara da tanadin ‘Fiquhussunah Jizu’i’ lamba ta 2 shafi na 362.