Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ƙuduri aniyar ganin an kammala babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, da Zaria zuwa Kano cikin watanni 14.
Yayin duba aikin a Tafa, a Jihar Neja, ya ce an soke kwangilar farko da aka bai wa kamfanin Julius Berger Plc saboda jinkiri da ƙarin farashi daga Naira biliyan 797 zuwa tiriliyan N1.5.
Don hanzarta kammalawa, aikin yanzu an rarraba shi zuwa rukuni uku.
- Da Yiwuwar Wasu Gwamnoni 5 Su Sauya Sheka Kafin Zaben 2027
- Rikicin Masarautar Kano Ya Sake Daukar Sabon Salo
Ministan Ayyuka, Sanata Dave Umahi, ya ce sabon kuɗin kwangilar Naira biliyan 252.89 ne, bayan amincewar Hukumar Sayayya ta Gwamnati (BPP).
Aikin zai haɗa da titin kilomita 10.6 zuwa Filin Jirgin Mallam Aminu Kano, kilomita 5 zuwa Jihar Kogi, da shigar fitilun hanya na hasken rana don inganta titin kafin a miƙa shi karkashin tsarin kula da aiki.
Gwamnati ta jaddada cewa wannan wa’adi ba za a karya shi ba, saboda titin na da muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arziƙi, sauƙaƙa zirga-zirga, da inganta tsaro.
Shugaba Tinubu, ya ce wannan aikin yana cikin muhimmancin ginin kayayyakin more rayuwa don ci gaban al’umma.