Wata babbar kotu da ke Ogun ta yanke wa wani mutum mai suna Adelake Bara, hukuncin kisa ta hanyar rataya, sakamakon kashe matarsa mai suna Olaleye Oke, bisa zargin hulda da maza.
Kotun ta yanke wa Bara hukuncin kisa ta hanyar ratayar ne ranar Litinin din da ta gabata.
Mai shari’a Patricia Oduniyi wanda ya yanke hukuncin ya ce, kafin yanke wannan hukuncin sai da aka tabbatar da cewa, Bara ya aikata laifin da ake zarginsa da shi.
Tun da farko dai, lauyar gwamnatin jihar, Misis T.O Adeyemi, ta bayyana cewa, wanda aka yanke wa hukuncin ya tabbatar da aikata laifin da ake zarginsa da shi a Afodan da ke jihar Ogun.
Adeyemi ya ce, lokacin da aka kashe an same shi a gonarsa ne yana aiki, yayin da Bara ya same shi, ya tuhume shi da laifin neman matarsa. Bara dai yana da mata uku, saboda haka ana cikin wannan takaddama sai ya dauko bindiga ya harbe Oke, bayan aikata wannan mummunan aiki, ya yi yunkurin gudu amma dai hakan ba ta yiwu ba, don haka ya shiga hannu, zai girbi shukar da ya yi.