Hukumar kula da sararin samaniya ta Nijeriya (NiMet), a cikin sabon hasashenta, ta ce za a yi ruwan sama kamar da bakin kwarya na kwanaki hudu a jihohi biyar na arewacin kasar, da kuma babban birnin tarayya Abuja.
Jihohin da mamakon ruwan saman zai shafa sun hada da wasu sassan Kaduna, Neja, Bauchi, Filato, Nasarawa, da kuma babban birnin tarayya Abuja.
Acikin rahoton kuma, NiMet ta bayyana cewa ana sa ran za a samu ruwan sama matsakaici a jihohi kamar Kwara, Oyo, Kogi, Ogun, Ekiti, Ondo, Sokoto, Katsina, Zamfara, Kebbi, Kano, Jigawa, Yobe, Borno, Gombe, Adamawa, Taraba, Benue, Cross River, Akwa Ibom, Ebonyi, Enugu, Abia, Imo, Anambra, Rivers, Edo da Delta.
Rahoton ya ce ana sa ran samun ruwan sama jefi-jefi zuwa matsakaici a sauran sassan kasar nan a cikin wa’adin da aka yi nazari akai.
Don haka, An yi hasashen yiwuwar afkuwar ambaliyar ruwa a kan tituna, da kananan matsuguni da magudanun ruwa a yankunan da Ruwan Saman zai sauka da yawa.
“Saboda haka, ana shawartar jama’a da su guji zama a magudanun Ruwa, kar su shiga hanyar ruwa mai malala da karfi,” Inji sanarwar.