• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Za A Sake Yin Gasar Masu Kirkira Da Fasaha Ta Katsina Karo Na Biyu

by El-Zaharadeen Umar
3 years ago
Gasa

Kwamitin gudanar da gasar masu kirkira da fasaha da suka shafi fannoni daban daban a jihar Katsina wanda ake kira Katsina national talent hurt Challenge’a turance ya bada sanarwar yin gasar karo na biyu.

Shugaban kwamitin gasar Arch Mansur Kurfi ya bayyana haka a lokacin taron manema labarai da kwamitin ya kira wanda ya bayyana cewa sun kammala duk wasu shirye-shirye na fara gasar

Arch Mansur Kurfi ya ƙara da cewa wannan gasa ɗaya ce daga cikin ƙoƙarin gwamna Aminu Bello Masari wanda ya yarda tare da girmama mutane masu fasaha da kirkira domin ba su dama su baje kolin baiwar da Allah ya yi masu a wannan gasar wanda hakan zai ƙara ba wasu dama.

Ya ƙara da cewa idan za a iya tunawa kashin farko na wannan gasa an yi shi ne a farkon wannan shekara ta 2022 inda fiye da mutane 7,000 suka shiga wannan gasa kuma aka tantance mutum 250 sannan daga ƙarshe mutum 13 suka samu nasara a bangarori daban daban.

A cewar sa, mutane 13 sun samu kyaututuka da dama da suka haɗa da naira miliyan ɗaya da rabi zuwa naira miliyan biyar ya yin da wanda ya zo na ɗaya ya samu mota kira Toyota Highlander da kuma kuɗi miliyan biyu.

LABARAI MASU NASABA

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

Ya cigaba da cewa an zaɓi mutane 100 daga cikin waɗanda suka shiga gasar inda kowanensu aka bashi Naira dubu ɗari, ya ƙara da cewa ko ba komi jihar Katsina ta amfana da wannan gasa inda aka samar da wani ɓangare na koyan ƙere-ƙere a kwalejin Hassan Usman Katsina

Arch Mansur Kurfi ya yi ƙarin haske akan wannan gasa ta bana inda ya ce bangarori huɗu ne za a shiga gasar akan su kuma za a fitar da mutane uku daga kowane fanni da kuma wanda ya zo ɗaya.

“Ɓangarori sun haɗa da na farko kwarewa akan zane na biyu gyaran mota na uku kuma fasaha akan Na’ura mai ƙwaƙwalwa da kuma fannin waka da Kiɗa waɗannan sune bangarori guda hudu da za a kafsa akan su insha’Allahu” inji shi

Ya ce domin ba kowane matashi damar shiga wannan gasa tuni an fara bayar da fom ɗin shiga wannan gasa, ga waɗanda ke da sha’awa shiga za a yi zuwa ofishin wannan cibiyar da ke Khallilul Rahama Plaza ko kuma ta hanyar ziyartar yanar gizo www.katsinanationaltalebthurtchallege.org domin yin rijista.

Daga ƙarshe ya bayyana fatan da yake da shi cewa matasa masu fasaha da kirkira za su shiga wannan gasa a dama da su a wannan baje kollin masu basira da baiwa karo na biyu da zai gudana a jihar Katsina

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati
Labarai

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025
An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba
Labarai

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta
Manyan Labarai

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Next Post
Babban kalubalen Majalisar Dokokin Nijeriya A Yanzu – Sanata Barkiya

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.