Fadar Vatican ta tabbatar da cewa a ranar Asabar za a gudanar da jana’izar Fafaroma Francis a babbar cocin St. Peter’s Basilica.
Wannan na zuwa ne bayan rasuwarsa a safiyar ranar Litinin yana da shekaru 88, sakamakon rashin lafiyar da ta haɗa da bugun zuciya da kuma matsalar jiki.
- Shettima Ya Gayyaci Shugaban NAHCON Da Mambobin Hukumar Kan Shirye-shiryen Hajjin 2025
- Yadda Aka Yi Zanga-zanga Kan Matsalar Tsaro A Filato
Fafaroma Francis ya kwashe makonni a asibiti a farkon shekarar nan saboda cutar numfashi, amma ya samu sauƙi ya koma gida.
Ya shafe shekaru 12 yana zaune a Santa Marta a matsayin Fafaroma, inda kuma gawarsa ke kwance yanzu.
Fadar Vatican ta ce manyan limaman cocin Katolika, wato Cardinals, za su yi taro domin shirya jana’izar, tare da shirin zaɓen sabon Fafaroma a watan da ke tafe.
Wasu shugabannin duniya da suka bayyana niyyarsu ta halartar jana’izar sun haɗa da Donald Trump na Amurka, Emmanuel Macron na Faransa, Luiz Inacio Lula da Silva na Brazil, da Volodymyr Zelensky na Ukraine.
Ana sa ran jana’izar za ta samu halartar manyan baƙi daga sassan duniya, tare da girmama rayuwar Fafaroma Francis da ayyukansa da ya yi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp