Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya shelanta cewa daga yanzu duk wani mutumin da ‘yan bindiga suka kashe a jihar za a bai wa iyalansa tallafin Naira miliyan daya, idan mace ce ko karamin yaro za a ba su Naira 500,000.
Kazalika, wannan tallafin a cewar gwamnan zai shafi dukkanin wani jami’in tsaron da ya rasa ransa a fagen fafatawa da masu garkuwa da mutane.
- Kisan Lauya: Gwamnan Legas Ya Gana Da Sufeton ‘Yansanda
- Zan Fi Mayar Da Hankali Kan Ilimi Da Matasa – Kwankwaso
Bala, ya shaida hakan ne a lokacin da ke jawabi a fadar hakimin kasar Duguri da ke karamar hukumar Alkaleri a wata ziyarar jajanta wa al’ummar yankin da ‘yan bindiga suka kashe mutane sama da 20 a baya-bayan nan.
Ya ce, “Kuma daga yanzu saboda da tausayawa duk wanda ya rasa ransa a Jihar Bauchi, za a bai wa iyalansa miliyan daya, idan mace ce za a ba ta dubu dari 500, idan yaro ne dubu dari 500.
“Wannan tallafi ne bai isa diyya ba.
“Mun rasa mutane a nan, mun rasa mutane a Toro mun kuma rasa mutane a sauran wurare; ga shugaban karamar hukumar za mu kidaya mutanen da suka rasu mu yi kokari mu ba su tallafi, saboda masu kawo abinci su suka rasu.
“Sannan da sauran jami’an tsaro da suka rasa rayukansu su ma za mu basu wannan tallafin da ‘yansanda kuma da ‘yan banga.
“Saboda haka ku fito yi ts ranku, ku fito ku yi yaki, mu ba a sanmu a ragonta ba. Ba wai daga Zamfara mutum ya zo ba, ko daga birnin Sin yake ba za mu bar shi ba.
“Muna rokon shugaban ‘yan sanda ya gina mana ofishin’yansanda a wannan garin, mu za mu gina shi kuma ya turo muku ‘yansanda.
“Amma kun san idan babu hanya ba zai ji dadin aiki ba, don haka muna tunanin yadda za a samar da hanyoyi kuma in sha Allahu za a yi.
“A madadin gwamnati da al’ummar Jihar Bauchi, na zo nan ne domin na jajanta muku bisa kashe mutane da aka yi da kone gidaje da ‘yan bindiga suka yi, Allah ya ba da hakuri, Allah ya ba da hakuri.
“Duk Wani dan bindiga da kuka gani a yankunku ku kashe shi. Na nada wannan umarnin kuma babu wata yafiya. Ba za mu bari mu ci gaba da asarar mutanenmu haka nan ba.
A kwanakin baya ne mahara suka kai hari yankin Alkaleri s jihar, inda suka kashe sama da mutum 20.